'Dalibai Sun Yi Wa Mataimakiyar Gwamna Rubdugu da Sanduna, Ta Sha da Ƙyar
- Mataimakiyar gwamnan jihar Ogun, Injiniya Noimot Salako-Oyedele, ta tsallake wani hari da dalibai masu zanga-zanga suka kai mata a Abeokuta
- Daliban sun lalata wasu motocin ayarin Salako-Oyedele, tare da jikkata wasu jami’an tsaro da ke kokarin shawo kansu
- Mataimakiyar gwamnan ta ba da umarnin janye ayarinta don kauce wa kara tsanantar rikicin kuma hakan ya taimaka wajen kare rayuka da rage cunkoso
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Ogun - Mataimakiyar gwamnan jihar Ogun, Injiniya Noimot Salako-Oyedele, ta tsallake wani mummunan hari daga wasu dalibai da suka fito zanga-zanga.
Lamarin ya faru ne ranar Laraba, 15 ga watan Janairu, 2025 a Abeokuta, babban birnin jihar Ogun da ke Kudu maso Yammacin Najeriya.
Mstaimakiyar gwamna ta tsallake hari
Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa ɗaliban sun farmaki ayarin mataimakiyar gwamnan ne a kan hanyar zuwa sansanin sojoji na 35 Artillery Brigade da ke Alamala.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Salako-Oyedele na hanyar zuwa sansanin sojojin domin wakiltar Gwamna Dapo Abiodun a bikin tunawa da gwarazan sojojin Najeriya na wannan shekara, 2025.
Daliban, waɗanda aka ce sun fito ne daga kwalejin fasaha ta Moshood Abiola (MAPOLY), sun tsunduma zanga-zangar ne bisa dalilin da ba a bayyana ba.
Sai dai an tattaro cewa ɗaliban na ɗauke da sanduna da wasu kayayyaki masu haɗari a lokacin zanga-zangar wacce ake tsammanin ta lumana ce.
Ɗalibai sun tare ayarin mataimakiyar gwamna
A lokacin da ayarin mataimakiyar gwamnan ya isa wurin zanga-zangar, daliban sun toshe hanyar da za ta bi tare da kokarin hana motocin su wuce.
Duk da ƙoƙarin da jami’an tsaro suka yi, daliban sun ƙi bada hanya kuma suna gane mataimakiyar gwamna ce sai suka fara farmakar motocin da sanduna.
Wasu daga cikin daliban sun farmaki motocin jami'an tsaron ayarin, suka lalata su kuma suka ji wa wasu dakaru rauni.
Mataimakiyar gwamnan Ogun ta janye ayarinta
Domin kaucewa ƙarin tashin-tashina, Salako-Oyedele ta umarci ayarinta su koma gidam gwamnati don ba ɗaliban damar wucewa lafiya.
Wannan matakin ya taimaka wajen rage tasirin rikicin da kuma kare rayukan wadanda ke cikin ayarin.
Zanga-zangar ta jawo cunkoson ababen hawa
Zanga-zangar ta jawo cikas ga zirga-zirgar ababen hawa a yankin, tare da haifar da lalacewar wasu motocin tsaro da kuma raunuka ga jami’an tsaro.
Duk da haka, jami'an tsaro sun tabbatar da cewa mataimakiyar gwamnan ta tsallake lafiya ba tare da wani rauni ba.
Babu wata sanarwa daga daliban MAPOLY ko hukumomin jami’a dangane da wannan lamarin.
Sai dai, ana sa ran gwamnatin jihar Ogun za ta ɗauki matakan da suka dace domin tabbatar da cewa irin wannan lamarin bai sake faruwa ba a nan gaba.
Ƴan daba sun farmaki Majalisa a Ogun
A wani labarin, kun ji cewa kansiloli sun barke da rikici kan zaben shugabanni a majalisar ƙaramar hukumar Abeokuta da ke jihar Ogun.
Ana tsakiyar wannan rigimar ne wasu matasa da ake zargin 'yan daba ne suka kutsa majalisar tare da sace sandar girma.
Asali: Legit.ng