Rundunar Sojoji Ta Hana Amfani da Jirage Marasa Matuka, Ta Fadi Dalili

Rundunar Sojoji Ta Hana Amfani da Jirage Marasa Matuka, Ta Fadi Dalili

  • Rundunar sojojin Operation Hadin Kai ta haramta yin amfani da jirage marasa mayuƙa a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya
  • Kwamandan sashen sama na rundunar wanda ya sanar da hakan, ya ce amfani da jiragen na kawo barazana ga tsaro
  • Air Commodore U.U Idris ya koka kan yadda wasu hukumomin gwamnati ke amfani da jiragen ba tare da bin ƙa'idoji ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Rundunar haɗin gwiwa ta Operation Hadin Kai, ta koka kan amfani da jirage marasa matuƙa a yankin Arewa maso Gabas.

Rundunar sojojin ta haramta yin amfani da jiragen marasa matuƙa a yankin Arewa maso Gabas na Najeriya.

Rundunar sojoji ta hana amfani da jirage marasa matuka
Rundunar sojoji ta haramta amfani da jirage marasa matuka a yankin Arewa maso Gabas Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa kwamandan sashen sama na rundunar, Air Commodore U.U. Idris, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: An shiga jimami bayan dan takarar PDP ya rasu ana daf da zabe

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Meyasa aka hana amfani da jiragen?

Kwamandan ya bayyana cewa amfani da jirage marasa matuƙan ba tare da izini ba yana haifar da barazana a jihohin Borno, Yobe da Adamawa.

Ya koka kan yadda hukumomin gwamnati da masu zaman kansu ke amfani da jirage marasa matuƙa ba tare da samun izinin sashen sama na rundunar Operation Hadin Kai ba.

"Yawaitar amfani da jirage marasa matuƙa don harkokin ƙashin kai ko kasuwanci ya jawo damuwa sosai dangane da tsaro."
"Wannan fargabar ta ta'allaƙa ne musamman ga yiwuwar ƴan tada ƙayar baya da wasu miyagu su yi amfani da su don ayyukan tayar da hankali ko kai hare-hare."
"Abin damuwa shi ne yadda hukumomin gwamnati da masu zaman kansu ke amfani da jirage marasa matuƙa ba tare da la'akari da dokoki da ƙa'idojin da ke jagorantar amfani da su ba."
"Haka kuma, ƴan tada ƙayar baya sun ƙware sosai wajen amfani da jiragen domin kai hari ga sojoji da muhimman wuraren ƙasa, kamar yadda suke gani a wasu wuraren."

Kara karanta wannan

Saurayin da ya yanke wuyan budurwarsa 'yar NYSC ya ce bai yi nadama ba

"Kwanan nan, rundunar ta samu rahotannin ganin jirage marasa matuƙa da amfani da su ba bisa ƙa'ida ba."
"A ranar 7 ga Janairu, 2025, an kama wani fasinja a cikin jirgin wata ƙungiyar agaji daga Maiduguri zuwa Monguno da jirgi mara matuƙi yayin bincike a filin jirgin sama."
"An kwace jirgin, kuma ana ci gaba da bincike. Wannan lamarin tare da wasu, ya nuna yadda mutane ke ƙoƙarin amfani da jiragen wanda hakan ke haifar da illa mai girma."
"Saboda haka, ya zama dole a sake jaddada haramcin amfani da jiragen a yankin Arewa maso Gabas kamar yadda hukumomi suka yi umarni."
"Ya kamata a fahimci cewa idan aka saɓa wannan haramcin, komai ƙanƙantar shi, za a ɗauki matakin da ya dace."

- Air Commodore U.U. Idris

Sojoji sun kashe ƴan bindiga a Zamfara

A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun sojojin Najeriya sun samu nasara kan ƴan bindiga masu addabar mutane a jihar Zamfara.

Kara karanta wannan

Gwamnoni 6 sun ajiye siyasa gefe, sun ɗauki matakin kare jihohinsu daga ƴan ta'adda

Sojojin sun hallaka ƴan bindigan guda biyu waɗanda suka takurawa wasu ƙauyuka na ƙaramar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng