Tirkashi: Hukumar Kwastam Ta Kwace Motoci 397 da Kudinsu Ya Haura Naira Biliyan 5

Tirkashi: Hukumar Kwastam Ta Kwace Motoci 397 da Kudinsu Ya Haura Naira Biliyan 5

  • Hukumar hana fasa kwauri ta Najeriya (Kwastam) ta ce ta kama motoci 397 da darajarsu ta kai Naira biliyan 5.64 a shekarar 2024
  • Kwastam ta ce ta kama magungunan jabu da darajarsu ta kai Naira biliyan 3.04 da shinkafa buhu 183,527 don kare tattalin arziki
  • Hukumar ta bayyana yadda ta yi haɗin gwiwa da ƙasashen duniya wajen tunkarar ƙalubalen fasa kwauri a iyakokin Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Adewale Adeniyi, shugaban hukumar Kwastan ta Najeriya (NCS), ya bayyana cewa an kama motoci 397 da darajarsu ta kai Naira biliyan 5.64 a 2024.

A yayin wani taron manema labarai a Abuja, Adeniyi ya ce dabarun aiwatar da dokokin hukumar sun haɗa da tsaron ƙasa da yarjejeniyoyin ƙasa da ƙasa.

Shugaban hukumar Kwastam ya yi magana kan nasarorin da suka samu a shekarar 2024
Hukumar Kwastam ta kama motocin Naira biliyan 5.64 da bindigogi, magunguna da sauransu a 2024. Hoto: @CustomsNG
Asali: UGC

A cikin rahoton taron da jaridar The Cable ta fitar, shugaban hukumar ta Kwastam ya ce:

Kara karanta wannan

Tinubu ya jaddada shirin ragargazar 'yan ta'adda a fadin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Mun kama motoci 397 da darajarsu ta kai Naira biliyan 5.64 don tabbatar da dokokin shigo da kaya da kare kuɗaɗen gwamnati."

Kwastam ta kama kayayyakin laifi a 2024

Adeniyi ya ce ƙwarewar masu fasa kwauri na haifar da bukatar ƙarin dabaru a cikin hukumar, ciki har da haɗin gwiwa da ƙasashen duniya da amfani da sababbin fasahohi.

Ya ce hukumar ta NCS ta gyara dabarunta don magance matsalolin tsaro da ke tasowa, wanda ya kai ga kama kayayyaki 3,555 a shekarar 2024.

"An samu ƙaruwar kaso 100.92% na kuɗin harajin (DPV) da aka biya akan kayan da aka kama, daga Naira biliyan 17.56 a 2023 zuwa Naira biliyan 35.29 a 2024."

- A cewar Adewale Adeniyi.

Adeniyi ya bayyana cewa kudaden kayayyakin da aka kama sun kai Naira biliyan 28.46, yayin da kudin harajinsu ya kai Naira biliyan 6.83.

Jami'an kwastam sun kama bindigogi, magunguna

Shugaban hukumar na Kwastam ya ci gaba da cewa:

Kara karanta wannan

"Ku ɗauki matakan kariya," An tabbatar da ɓullar sabuwar cuta mai tsanani a Kano

"An kama bindigogi 900 da harsasai 113,472, wanda ya haɗa da kama miyagun ƙwayoyi da magunguna da ba a amince da su ba."

Hukumar ta bayyana cewa an kama magunguna 175,676 da kwantena 6,271 na jabun magunguna da darajarsu ta kai Naira biliyan 3.04.

An yi kira ga al’umma su fahimci rawar da NCS ta ke takawa wajen kare lafiyar jama’a daga barazanar jabun magunguna da miyagun ƙwayoyi.

Adeniyi ya kuma bayyana cewa an kama kayan dabbobi da na namun daji guda 76 da darajarsu ta kai Naira biliyan 5.93.

Hukumar kwastam ta sha alwashin kare tattali

A cewar Adeniyi, an kama buhunan shinkafa 183,527 don tabbatar da tsaron kasuwar cikin gida da tallafawa tsarin gwamnatin Najeriya na bunkasa tattalin arziki.

Hukumar ta kuma samu nasarar kama kayan da aka hana shigowa da su, ciki har da yadi guda 3,785 da darajarsu ta kai Naira miliyan 945.9.

An kuma kama takalma, abin sha, da wasu kayan masarufi na daban, wanda hakan ya taimaka wajen kare masana’antu da tallafawa bunkasa tattalin arzikin gida.

Kara karanta wannan

Kayayyakin miliyoyin naira sun kone bayan tashin gobara a fitacciyar kasuwa

Hukumar kwastam ta sha alwashin cigaba da tunkarar duk wani ƙalubale da ke da alaka da fasa kwauri domin tabbatar da tsaron ƙasa da tattalin arziki.

Mutane 573,519 suka nemi aikin Kwastam

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar Kwastam ta Najeriya (NCS) ta ce mutane 573,519 ne suka nemi guraben aiki 3,927 da aka buɗe na zangon 2024/2025.

Ministan Kuɗi, Olawale Edun, ya tabbatar da amincewar gwamnati kan ɗaukar ma’aikata 3,927 a hukumar Kwastam amma adadin da suka nemi aikin ya ba da mamaki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.