Tawagar Sojoji Ta Sauka a Zamfara bayan Harin da Ya Kashe Bayin Allah
- Sojojin Sama na Najeriya sun aika wata tawaga zuwa Zamfara don fara bincike kan harin da sojoji suka kai wa al’ummar jihar
- Ana zargin sojojin da kai harin bama bisa kuskure, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu mazauna wani gari, Tungar Kara
- Tuni dai Zamfara don yi wa iyalan wadanda abin ya shafa ta’aziyya da kuma gudanar da bincike a kan yadda aka tafka kuskuren
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Zamfara - Sojojin Sama na Najeriya sun aika wata tawaga zuwa Zamfara don fara bincike kan harin da sojoji suka kai wa al’ummar jihar bisa kuskure.
Ana zargin Sojojin Sama na Najeriya da yin harin bama-bamai bisa kuskure, wanda ya yi sanadin mutuwar wasu mazauna garin Tungar Kara a karamar hukumar Maradun.

Kara karanta wannan
ICPC ta sake cafko wani mutumin El Rufa'i, za a tafi kotu da shi kan zargin rashawa

Asali: Facebook
AIT ta ruwaito cewa wata tawaga karkashin jagorancin Daraktan Tsare-tsare da Hadin Gwiwa na sashen hulda tsakanin sojojin, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, ta jagoranci wannan ziyara.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojoji sun yi ta'aziyyar mutanen Zamfara
Tawagar Sojojin Sama ta isa jihar Zamfara don yi wa iyalan wadanda abin ya shafa ta’aziyya da kuma gudanar da tantancewa don kauce wa sake afkuwar irin wannan matsala a nan gaba.
Dakarun sojoji na ci gaba da kai hare-hare kan ‘yan ta’adda da ke addabar fararen hula a jihar Zamfara, inda suke kashe da dama daga cikinsu.
A cikin wannan aiki ne suka kai harin bam bisa kuskure a garin Tungar Kara, karamar hukumar Maradun, inda wasu mazauna garin suka samu rauni ko rasa rayukansu.
Gwamna ya karbi tawagar sojojin sama
Gwamna Lawal ya yaba da ziyarar ta’aziyya da Sojojin Sama suka kai masa, yana mai bayyana hakan a matsayin jagoranci nagari, tare da yabawa da jajircewarsu wajen yaki da ‘yan ta’adda.
Ya bayyana cewa idan aka kawo karshen ta’addanci a jihar Zamfara, za a iya magance sama da 70% na matsalar ta'addanci da ta addabi Najeriya, musamman a Arewa.
Bayan tawagar ta kai ziyara ga Gwamnan da kuma hedikwatar rundunar Operation Fansan Yamma, sun wuce zuwa garuruwan da abin ya shafa.
Sun isa Tungar Kara da yankin Kakidawa na karamar hukumar Maradun, don yi wa iyalan wadanda abin ya shafa ta’aziyya da gudanar da bincike kan lamarin.
PDP ta yi takaicin harin sojin sama
Jam'iyyar PDP reshen jihar Zamfara ta shaida wa Legit cewa ta na sane da irin kokarin da rundunar sojin Najeriya ke yi wajen dawo da zaman lafiya zuwa jihar.
Kakakin jam'iyyar, Halliru Andi ya ce;
"Mu na kara kira gare su (sojoji) domin ganin an dauki kwararan matakai don kare afkuwar haka a nan gaba.
Jam'iyyar PDP reshen Zamfara, ta na jinjina fadi tashin sojojin Najeriya don maido da tsaro a jihar Zamfara.
An saki tsohon hadimin gwamnan Zamfara
A wani labarin, kun ji cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta bayar da umarnin sakin Bashir Hadejia, tsohon mai ba da shawara ta musamman ga tsohon Gwamnan Zamfara, Bello Matawalle.
Hadejia ya shigar da kara ta hannun lauyansa Mahmud Magaji, ya tuhumi Sufeto Janar na ‘Yan Sanda, DSS, da wasu manyan hafsoshin tsaro bisa zarginsa da laifin ta'addanci.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng