An Shiga Jimami bayan 'Dan Takarar PDP Ya Rasu Ana daf da Zabe
- Ajali ya cimma ɗan takarar kansila na jam'iyyar PDP a mazaɓar 01, Oloba/Atapara da ke ƙaramar hukumar Ede ta Arewa a jihar Osun
- Dauda Nurein ya rasu ne a yammacin ranar Talata, 14 ga watan Janairun 2025 bayan ya yi fama da ƴar gajeruwar jinyar rashin lafiya
- Jam'iyyar PDP ta yi alhinin rashin da aka yi na Dauda Nurein wanda ta bayyana a matsayin mutumin kirki
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Osun - Jam’iyyar PDP reshen jihar Osun ta shiga cikin jimami bayan rasuwar ɗan takararta na kujerar Kansila a mazabar 01, Oloba/Atapara, Ede ta Arewa, Dauda Nurein.
Dauda Nurein, wanda aka shirya zai tsaya takara a zaɓen ƙananan hukumomi na ranar 22 ga watan Fabrairu a inuwar PDP, ya rasu ne a ranar Talata bayan ya yi jinyar ɗan gajeren lokaci.

Kara karanta wannan
Ana shirin ƙara farashin fetur a Najeriya, NNPCL ya tara wa gwamnati Naira tiriliyan 10

Source: Facebook
An sanar da mutuwarsa ne a wani rubutu da hadimin gwamnan jihar Osun, Akintunde Bello Sheriff ya yi a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An yi alhinin rasuwar ɗan takarar PDP
A cikin saƙon ta’aziyyarsa, Akintunde Bello Sheriff ya bayyana matuƙar mamaki da baƙin ciki kan rasuwar Dauda Nurein.
"Kansilan da muke jira mu zaɓa a mazabata ya yi bankwana da duniya a yammacin ranar Talata bayan ƴar gajeruwar rashin lafiya."
“Mun girma tare a unguwarmu amma yanzu Nurein ya tafi. A karo na ƙarshe da muka haɗu, mun taru ne a gidan ɗan’uwanmu, Olugbenga Akanfe, lokacin shagulgulan sabuwar shekara."
"Ba mu taɓa ji a rai cewa lokacin Nurein a duniya ya kusa zuwa ƙarshe ba."
“Wannan labari ne mai matuƙar tayar da hankali ga mambobin PDP na Ede ta Arewa. Allah ya raya mu waɗanda muka rage. Ina yi maka bankwana Olobe Dauda Nurein. Allah ya gafarta maka."

Kara karanta wannan
Watanni bayan tausaya wa yan Najeriya kan halin kunci, yar Majalisar Tarayya ta rasu
- Akintunde Bello Sheriff
PDP ta yi ta'aziyyar rasuwar ɗan takarar kansila
Jaridar The Punch ta rahoto cewa kakakin jam'iyyar PDP a jihar Osun, Oladele Bamiji, ya nuna alhininsa kan rasuwar Dauda Nurein.
"Marigayin yana da matuƙar farin jini. Duk wanda ya gan shi ya san haka daga yadda mutane ke nuna ƙaunarsu gare shi."
"Allah Ya ba shi hutu na har abada Ya kuma albarkaci iyalansa da ya bari. Dukkanin iyalan PDP sun shiga jimami da alhini."
- Oladele Bamiji
Rasuwar Nurein ta jefa jam’iyyar PDP a Osun cikin baƙin ciki, musamman a Ede ta Arewa, inda aka san shi sosai kuma ake ganin girmansa.
Wannan mummunan labari ya kasance babban rashi ga jam’iyyar, musamman ganin cewa ana sa ran zai taka muhimmiyar rawa a zaɓen ƙananan hukumomi da ke tafe.
Tsohon gwamnan Sokoto ya fice daga PDP
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Sokoto, Dalhatu Attahiru Bafarawa, ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar PDP mai adawa a Najeriya.

Kara karanta wannan
Daga karshe Isra'ila da Hamas sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, bayanai sun fito
Tsohon gwamnan na jihar Sokoto ya sanar da ficewar ta sa ne a cikin wata wasiƙa da ya rubuta zuwa ga shugaban jam'iyyar PDP na ƙasa.
Alhaji Bafarawa ya bayyana cewa ya ɗauki matakin mai tsauri ne domin yana so a maida hankali kan wasu abubuwa da suka shafi rayuwarsa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng