"Ku Maida Hausa Yaren Koyarwa a Makarantu," Gwamna Ya ba Gwamnonin Arewa Shawara

"Ku Maida Hausa Yaren Koyarwa a Makarantu," Gwamna Ya ba Gwamnonin Arewa Shawara

  • Gwamnan Neja, Mohammed Umaru Bago, ya yi kira ga gwamnonin jihohin Arewa su yi amfani da Hausa a matsayin harshen koyarwa a makarantu
  • A cewar Gwamna Bago, Turanci ya kamata ya zama darasi ne kawai a makarantun firamare da sakandare a Arewa, ba harshen koyarwa ba
  • Gwamnan ya kuma bayyana cewa wannan mataki zai taimaka wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a yankin Arewa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Gwamnan jihar Neja, Mohammed Umaru Bago, ya bukaci takwarorinsa gwamnoni a jihohin Arewa su sake duba tsarin karatun makarantu.

Gwamna Bago ya shawarci gwamnonin Arewa su rungumi amfani da Hausa a matsayin harshen koyarwa a yankin.

Gwamna Bago.
Gwamna Bago ya shawarci gwamnonin Arewa su maida Hausa ya zama yaren koyarwa a makarantu Hoto: @Bagoforgovernor
Asali: Twitter

Gwamnan ya ce kamata ya yi Turanci ya kasance a matsayin darasi kawai a makarantun firamare da sakandare a Arewa, ba matsayin yaren koyarwa ba, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Dan takarar PDP ya tayar da kura, ya amince gwamnan APC ya yi tazarce a 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bago ya faɗi haka ne a taron "National Literary Colloquium" domin bikin cikar fitaccen marubuci, BM Dzukogi, wanda ya kafa gidauniyar Hilltop Arts, shekara 60 da haihuwa.

Taron ya gudana a cibiyar taro ta ƙasa-da-ƙasa ta Mai shari'a Idris Legbo Kutigi da ke Minna, babban birnin jihar Neja.

Gwamna Bago ya nemi canza yaren koyarwa

Gwamna Bago ya ce idan aka maida Hausa a matsayin yaren koyarwa a makarantu, hakan zai karfafa shiga makarantu tare da saukaka fahimta ga ɗalibai.

A cewarsa, ya kamata gwamnonin Arewa su yi la'akari da wannan shawara don rage yawan yaran da ke gararamba a gari, ba sa zuwa makaranta.

Mohammed Bago ya ce amfani da Hausa zai samar da sauƙi wajen fahimtar darussa, musamman a yankunan da mafi yawan yara ba su da damar samun ilimi mai nagarta.

Wannan shawara, in ji shi, na da muhimmanci wajen rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta a Arewa, wanda ke ci gaba da zama babban kalubale.

Kara karanta wannan

Abba ya yabi jami'i mai amana, kwamitin rabon kayan makaranta ya maido rarar N100m

Gwamna ya ba iyaye shawara kan ilimi

Bugu da ƙari, gwamnan ya yi kira ga iyaye su ba wa ’ya’yansu kayan karatu da littattafai masu fa’ida don haɓaka tunaninsu da inganta iliminsu.

Ya bayyana cewa bunƙasa al’adar karatu na daya daga cikin hanyoyin ceto al’umma daga matsalolin lalacewar zamantakewa da ake fuskanta a yau.

Gwamna Bago ya kuma bayyana shirin gwamnatinsa na haɗa wasu makarantu wuri guda don koyar da ɗalibai sana'o'in da za su dogara da kansu, rahoton Daily Post.

Gwamnatin Neja za ta tallafawa matasa

Haka zalika, ya bayyana aniyar gwamnatinsa na yin hadin gwiwa da gidauniyar Hilltop Arts domin tallafa wa matasa da kuma inganta al’adun karatu a Najeriya gaba ɗaya.

Bago ya ƙara da cewa inganta harshen Hausa da kuma kyautata tsarin ilimi a yankin Arewa zai taimaka wajen ciyar da al’umma gaba tare da samar da mafita ga kalubalen jahilci da ake fuskanta.

Kara karanta wannan

Abba ya waiwayi daliban Kano, ya shirya yin abu 1 da zai ragewa iyaye kashe kudi

Gwamna Bago ya kafa tarihi a Neja

A rahoton kun ji cewa Gwamna Umar Bago ya gabatar da kasafin kuɗin da ba a taɓa ganin irinsa a Majalisar dokokin jihar Neja.

Umaru Bago, wanda ake wa take da manomin gwamna ya yi ƙiyasin kashe Naira tiriliyan 1.5 a shekarar 2025 da muka shiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262