Saurayin da Ya Yanke Wuyan Budurwarsa 'Yar NYSC Ya Ce bai Yi Nadama ba

Saurayin da Ya Yanke Wuyan Budurwarsa 'Yar NYSC Ya Ce bai Yi Nadama ba

  • Matashi ɗan shekara 32 mai suna Timileyin Ajayi ya amsa laifin kashe budurwarsa, Salome Adaidu wacce ke bautar ƙasa (NYSC) a Abuja
  • Timileyin Ajayi ya bayyana cewa bai yi nadama ba saboda ya yi hakan ne sakamakon zargin cin amanar da Salome Adaidu ta yi masa
  • 'Yan sanda a jihar Nasarawa sun tabbatar da cewa za su gurfanar da wanda ake zargin a kotu bayan kammala bincike domin masa hukunci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Nasarawa - Wani matashi ɗan shekara 32 mai suna Timileyin Ajayi, ya amsa laifin kashe budurwarsa, Salome Eleojo Adaidu, wacce ke bautar ƙasa a Abuja.

An kama Timileyin Ajayi a unguwar Papalana da ke New Karshi, karamar hukumar Karu, jihar Nasarawa, yayin da yake ƙoƙarin ɓoye sassan jikinta bayan ya kashe ta.

Kara karanta wannan

Bafarawa: Tsohon gwamnan jihar Sokoto ya fice daga jam'iyyar PDP, ya fadi dalili

Timileyin Ajayi
Saurayin da ya kashe budurwarsa ya ce bai yi nadama ba. Hoto: @african_glitz
Asali: Instagram

Channels TV ya ce an kama wanda ake zargin ne ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu, bayan wasu mazauna yankin sun gane shi yayin da yake ƙoƙarin watsa sassan jikin budurwarsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda saurayi ya kashe budurwarsa

Bayan kama wanda ake zargin, 'yan sanda sun gurfanar da shi a hedikwatar rundunarsu da ke Lafiya tare da makamai da suka haɗa da wuka da adda waɗanda ya yi amfani da su.

A yayin amsa tambayoyi, Punch ta wallafa cewa Timileyin ya tabbatar da cewa ya kashe Salome ne saboda ya gano tana cin amanarsa.

“Na kashe ta ne saboda ba ma tare da juna a ko da yaushe, ba wani abu da na shirya ba ne. Amma na gano tana hulɗa da wasu maza ta wayarta, kuma hakan ya fusata ni.”

- Timileyin Ajayi

"Bai yi nadama ba" – Timileyin Ajayi

Lokacin da aka tambaye Timileyin Ajayi ko ya yi nadamar kashe Salome, saurayin ya ce bai yi nadama ba.

Kara karanta wannan

"Soyayya ruwan zuma": Saurayi ya bankawa budurwarsa wuta, ya ce zai aure ta

“Ba na nadama saboda haka rayuwa take. Na yi hakan ne saboda na fahimci abin da take yi ya sabawa soyayyar gaskiya.
"Na yarda cewa mu biyun mun dace, amma ita tana cin amanar soyayyarmu,”

– Timileyin Ajayi

Martanin 'yan uwan Marigayi Salome

Esther Adaidu, wadda ita ce babbar 'yar uwar Salome, ta musanta sanin wata alaƙa tsakanin kanwar tata da wanda ake zargin.

Ta bayyana cewa iyalinsu ba su taɓa sanin Timileyin ba har sai lokacin da aka sanar musu da cewa ya kashe Salome.

'Yan Sanda sun yi alkawarin adalci

Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa, SP Ramhan Nansel, ya tabbatar da cewa za a yi adalci ga iyalan marigayiyar.

“Bincike na kan gaba, kuma bayan kammala binciken, za mu gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu.
"Muna kira ga duk wanda ke da ƙorafi kan wannan wanda ake zargin da ya gabatar mana da bayanan sa,”

Kara karanta wannan

An kama saurayin da ya yanke kan budurwarsa da wuka zai kai wa wata mata

- SP Ramhan Nansel

Haka zalika, ya bayyana cewa za a tabbatar an hukunta Timileyin idan aka tabbatar da laifin nasa a gaban kotu.

Iyalan Salome sun roƙi gwamnati da sauran hukumomin da ke da ruwa da tsaki a kan tabbatar da adalci da kuma hana irin wannan aika-aika faruwa a gaba.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa ta kama wani matashi bisa zargin kashe mahaifiyarsa.

Legit wallafa cewa matashin ya tabbatar da cewa shi da wani abokinsa suka hadu wajen kashe mahaifiyarsa suka wurga ta cikin rijiya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng