"Ku Ɗauki Matakan Kariya," An Tabbatar da Bullar Sabuwar Cuta Mai Tsanani a Kano
- Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta tabbatar da ɓullar cutar murar tsuntsaye mai tsanani wadda ke kama kajin gida da na turawa da ake kiwo
- Dr. Taiwo Olasoji ne ya tabbatar da haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, 14 ga watan Janairu a madadin babban likitan dabbobi na ƙasa
- Masana sun gargaɗi masu kiwon kaji su ɗauki matakan kariya domin daƙile yaɗuwar cutar zuwa jihohin maƙota
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano - Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da bullar cutar murar tsuntsaye mai tsanani (bird flu) a jihar Kano da ke Arewa maso Yammacin Najeriya.
Wannan murar tsuntsayen mai tsanani tana shafar nau'ikan tsuntsaye da dama, ciki har da kaji masu kwai, agwagi, farar hannu da kajin turawa da ba su ƙwai.
Jaridar Leadership ta ce gwamnati ta tabbatar da ɓullar cutar a Kano ne a wata sanarwa da Dr. Taiwo Olasoju ya fitar a madadin babban likitan dabbobi na Najeriya ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnatin tarayya ta nuna damuwa kan barazanar yaduwar cutar, musamman a wannan lokaci na farkon shekara.
Gwamnatin ta nemi a ɗauki matakan kariya
Sanarwar ta bukaci ofisoshin likitocin dabbobi na jihohi da hukumomin da abin ya shafa da su kara kaimi wajen sanya ido da aiwatar da tsauraran matakan kariya don dakile yaduwar cutar.
“Dole ne mu dauki matakan kariya masu kyau,” in ji sanarwar, tana mai kira ga masu ruwa da tsaki su haɗa kai don hana cutar yaduwa zuwa jihohi da yankunan makwabta.
Gwamnatin Najeriya ta kuma bada shawarar dagewa wajen wayar da kan jama’a tare da sanya ido kan dabbobin gida don gano da kuma magance sababbin cututtuka cikin gaggawa.
Shugaban PAN ya faɗi yadda aka gano cutar
Da yake karin haske kan lamarin, shugaban ƙungiyar masu kiwon kaji ta Najeriya (PAN), reshen Kano, Dr. Usman Gwarzo, ya bayyana yadda aka gano bullar cutar murar tsuntsayen ta farko.
Usman Gwarzo ya ce:
“A watan Disamba 2024, wani matashi daga unguwar Galadanchi a karamar hukumar Gwale ya sayi agwagwa daga kasuwar Janguza da ke karamar hukumar Tofa, ya kuma hada ta kajinsa da yake kiwo.
"Agwagar ta mutu ba zato ba tsammani, sai kuma kajin suka fara mutuwa ɗaya bayan ɗaya."
Ya kara da cewa an kai gawarwakin kajin asibitin dabbobi na Gwale, inda aka fara zargin cutar mura mai tsanani ta tsuntsaye (avian influenza).
Dr. Usman Gwarzo ya ce gwaje-gwajen da aka yi da samfurin sun tabbatar da ɓullar kwayar cutar a makon farko na watan Janairu 2025, rahoton Channels tv.
Ina mafita ga masu kiwon kaji a Kano?
Har yanzu dai ba a samu rahoton ɓullar wannan cuta daga gonakin kiwon kaji na kasuwanci ba, wanda hakan ya ba masu kiwon kaji kwanciyar hankali.
Masana sun shawarci masu kiwon kaji su mayar da hankali kan ɗaukar matakan kariya daga cututtuka, wanda ya haɗa da tsaftace kayan aiki, takaita shiga gonakin kaji, da zubar da waɗanda suka kamu.
Gwamnatin Tarayya musanta dawowar cutar korona
A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta musanta raɗe-raɗen da ake yaɗawa na bullar sabon nau'in cutar korona.
Ma'akkatar lafiya ta kwantar da hankulan ƴan Najeriya, tana mai cewa babu wata alama da ta tabbatar da shigowar cutar Najeriya.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng