Kayayyakin Miliyoyin Naira Sun Kone bayan Tashin Gobara a Fitacciyar Kasuwa

Kayayyakin Miliyoyin Naira Sun Kone bayan Tashin Gobara a Fitacciyar Kasuwa

  • Mummunar gobara da ta tashin a cikin tsakar dare a wata kasuwa da ke jihar Anambra, ta jawo asarar dukiya mai tarin yawa
  • Gobarar wacce ta tashi a cikin tsakar dare ta ƙone shaguna masu yawa tare da lalata kayayyaki na miliyoyin Naira
  • Hukumar kashe gobara ta jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin, ta ce ta tura jami'anta zuwa wurin domin kai agajin gaggawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Anambra - An samu tashin wata gobara da ta jawo asarar kayayyaki na miliyoyi a jihar Anambra.

Mummunar gobarar ta auku ne a kasuwar Ahịa Mgbede, da ke kusa da kasuwar sayar da kayan gyaran motoci a Nnewi, jihar Anambra.

Gobara ta tashi a Anambra
Gobara ta yi barna a kasuwar Anambra Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar The Punch ta ce gobarar wacce ta fara da tsakar dare, ta lalata shaguna da dama inda kayayyaki masu yawa suka ƙone.

Kara karanta wannan

"Ku yi fatali da APC," CUPP ta ba ƴan Najeriya shawara da mafita a zaben 2027

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda gobarar ta auku

Shaidu sun bayyana cewa gobarar ta ci gaba da tashi na tsawon lokaci kafin ƴan kwana-kwana su isa wurin, yayin da waɗanda abin ya shafa da sauran jama'a suka yi ƙoƙarin ceto abin da za su iya.

Ɗaya daga cikin waɗanda abin ya shafa, wanda aka bayyana sunansa da Uche, ya faɗi mummunan halin da suka shiga.

"Mun zo da safe muka tarar shagunanmu sun ƙone kurmus. Asarar ba za a iya ƙiyasta ta ba, kuma ta girgiza al’ummar kasuwar nan baki ɗaya."

- Uche

Ya ƙara da cewa har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba, amma ya bayyana cewa masu shaguna da dama sun yi asara mai tarin yawa.

Haka kuma, ya bayyana cewa wata mata da gobarar ta shafa, saboda tsananin baƙin ciki ta yi yunƙurin cutar da kanta, amma jama'a suka samu suka ba ta baki.

Hukumomi sun yi bayani

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Mutanen gari sun yi tara tara, sun kama babban mawaƙi ɗauke da kan mace

Hukumar kashe gobara ta jihar Anambra ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa da shugabanta, Chukwudi Chiketa, ya fitar.

"Hukumar kashe gobara ta jihar Anambra ta kai ɗauki kan wata gobara da ta tashi a kasuwar Ahịa Mgbede, da ke daf da kasuwar kayan gyaran motoci ta Uruagu Nnewi, a ƙaramar hukumar Nnewi ta Arewa."
"An samu kiran gaggawa da misalin ƙarfe 2:15 na daren ranar Litinin, 14 ga watan Janairu, 2025. Nan take aka tura jami’an kashe gobara tare da kayan aiki daga ofisoshin Nnewi da Ogidi zuwa wurin da gobarar ta tashi."
"Jami’anmu sun yi ƙoƙari wajen kashe gobarar, amma ta sake tashi daga baya da safe. Ana ci gaba da ƙoƙarin kashe gobarar gaba ɗaya.”

- Chukwudi Chiketa

Shugaban hukumar kashe gobarar ya tabbatar da cewa ba a samu asarar rai ba sakamakon aukuwar lamarin.

Ya kuma yi kira ga jama’a da su ɗauki matakan kare kansu daga gobara da kuma gaggauta sanar da hukumar idan gobara ta tashi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta yi magana kan kisan manoma 40, ta fadi abin da ya faru

Gobara ta tashi a kasuwar Sokoto

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin wata gobara a ɗaya daga cikin fitattun kasuwannin da ke jihar Sokoto.

Gobarar wacce ta tashi a kasuwar hatsi ta Kara da ke cikin birnin Sokoto, ta jawo asara mai yawa bayan ta lalata shagunan ƴan kasuwa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng