Gwamnatin Borno Ta Yi Magana kan Kisan Manoma 40, Ta Fadi Abin da Ya Faru

Gwamnatin Borno Ta Yi Magana kan Kisan Manoma 40, Ta Fadi Abin da Ya Faru

  • Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da kai harin ta'addanci da ƴan ta'addan Boko Haram/ISWAP suka yi kan manoma
  • Ta tabbatar da cewa an kashe manoma aƙalla 40 a lokacin harin yayin da ake ci gaba da neman mutanen da ba a gani ba
  • Gwamnatin ta yi kira ga jama'a da su daina zuwa wuraren masu hatsari waɗanda jami'an tsaro ba su ba da iznin a je ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Gwamnatin jihar Borno ta tabbatar da kisan manoma 40 da ƴan ta'addan ISWAP/Boko Haram suka yi a ƙaramar hukumar Kukawa.

Harin ta'addancin wanda ake zargin ƴan ta’addan ISWAP/Boko Haram ne suka kai a ranar Lahadi, ya kuma yi sanadiyyar ɓatan mutane da dama.

Gwamnatin Borno ta tabbatar da kisan manoma 40
Gwamnatin Borno ta yi Allah wadai da kisan manoma 40 da 'yan ta'adda suka yi Hoto: @ProfZulum
Asali: Original

Jaridar Daily Trust ta ce a wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai da tsaron cikin gida, Farfesa Usman Tar ya fitar, ya bayyana harin a matsayin aikin ta’addanci.

Kara karanta wannan

"Ku murkushe su": Zulum ya nemi agajin sojoji da ƴan bindiga suka kashe manoma 40

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zulum ya yi takaicin kisan manoma a Borno

Tar ya ce gwamnan jihar, Babagana Umara Zulum, ya yi Allah wadai da harin tare da kiran rundunar sojojin Najeriya da su bi sawu tare da kawar da masu aikata wannan laifin.

“A ranar Lahadi, 12 ga watan Janairu, 2025, wasu ƴan ta’adda da ake zargin Boko Haram/ISWAP ne sun kai hari kan wasu manoma da masu kamun kifi a ƙauyen Dumba, kusa da Baga, a ƙaramar hukumar Kukawa."
“An fara bincike kan yadda wannan al’amari ya faru. Rahoton farko ya nuna cewa an kashe aƙalla manoma 40, yayin da ake bibiyar inda waɗanda suka tsira daga harin suke don a haɗa su da iyalansu."
"Cike da alhini da baƙin ciki, na samu labarin wannan harin a Dumba, inda ƴan ta’adda suka kashe manoma da masu kamun kifi da dama. A madadin gwamnati, ina mika ta’aziyya ga iyalan mamatan."
“Ina tabbatarwa al’ummar Borno cewa za a gudanar da bincike mai zurfi kan wannan lamari domin ɗaukar matakan da suka dace."

Kara karanta wannan

Boko Haram sun mamaye kauye suna harbi, sun kashe manoma 40

"Ina amfani da wannan dama domin kira ga rundunar sojoji da su bi sawun masu aikata wannan mummunan aiki kuma su hukunta su yadda ya kamata."
“An lura cewa manoman sun fita daga wuraren da hukumomin tsaro suka yarda a bi, suka shiga wuraren da ba a kammala tsaftace su ba."
"Irin waɗannan wuraren galibi suna fuskantar hare-haren dare daga ƴan ta’adda da kuma kasancewa ɗauke da bama-baman da aka binne a ƙarƙashin ƙasa."
"Gwamna Zulum ya yi kira ga jama'a da ka da su fita daga wuraren da jami'an tsaro da gwamnati suka tantance tare da amincewa su bi."

- Farfesa Usman Tar

Ƴan ta'addan Boko Haram sun kai hari a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa ƴan ta'addan Boko Haram sun kai wani hari a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Gwoza ta jihar Borno.

Ƴan ta'addan sun hallaka mutum biyu a yayin harin da suka kai yayin da suka ƙona gidaje da shaguna masu tarin yawa a ƙauyen.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng