'Yan Ta'addan Boko Haram Sun Kai Hari a Borno, Sun Yi Barna Mai Yawa
- Ƴan ta'addan Boko Haram sun yi ta'asa a jihar Borno bayan sun kai wani harin ta'addanci a ƙaramar hukumar Gwoza
- Miyagun ƴan ta'addan a harin da suka kai a ƙauyen Bamzir sun hallaka mutane biyu tare da raunata wata mata
- Shugaban ƙaramar hukumar Gwoza ya nuna alhininsa kan harin tare da jajantawa iyalan mutanen da suka rasa rayukansu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Borno - Ƴan ta’addan Boko Haram sun kai harin ta'addanci a wani ƙauye da ke jihar Borno.
Ƴan ta'addan a yayin harin da sukai a ƙauyen, sun hallaka mutum biyu tare da ƙona wata coci.
Ƴan Boko Haram sun kai hari a Borno
Tashar Channels tv ta ce harin an kai shi ne a ƙauyen Bamzir, wanda yake ƙarƙashin gundumar Whuntaku, a ƙaramar hukumar Chibok.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da tawagar yaɗa labarai ta shugaban karamar hukumar Chibok, Mustapha Madu ta fitar, ta tabbatar da aukuwar lamarin.
Sanarwar ta ce yan ta’addan sun kai harin da misalin ƙarfe 2:10 na tsakar daren ranar Lahadi, inda suka bankawa gidaje da dama wuta.
Hakan ya haifar da mutuwar wasu ƴan uwa biyu da aka bayyana sunayensu da Josiah Pogu Pudza, ɗalibi ɗan ajin SS2, da Enoch Pogu Pudza. Yayin da wata mai suna Esther Yohanna ta samu rauni sakamakon harbin bindiga.
Sanarwar ta bayyana cewa ƴan ta’addan sun kwashe kayan abinci da dabbobi, sannan suka ƙona ɗakin taro na cocin EYN LCC da gidaje da shaguna da dama.
Shugaban ƙaramar hukumar Chibok, Mustapha Madu, ya halarci jana’izar mutane biyun da aka kashe tare da nuna alhini ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.
Shugaban ƙaramar hukumar ya kuma duba duk wuraren da aka ƙona da suka haɗa da gidaje, shaguna, da kuma ɗakin taro na cocin da aka lalata.
Ƴan ta'adda sun yi ta'asa a Kebbi
Harin ya faru a lokacin da wasu da ake zargin ƴan ta’addan Lakurawa ne suka kashe mutane da dama a jihar Kebbi da ke yankin Arewa maso Yamma.
A harin na Kebbi, an kashe ma’aikatan sadarwa biyu da wani ɗan asalin kauyen Gumki da ke karamar hukumar Arewa.
Wadannan hare-hare na kara nuna irin matsalar tsaro da ake fuskanta a wasu sassan Najeriya, musamman a Arewa, inda al’ummomi da dama ke fama da hare-haren ƴan ta’adda.
Gwamnati da hukumomin tsaro sun sha alwashin yin duk mai yiwuwa don ganin an kawo ƙarshen ƙalubalen rashin tsaro.
Ƴan ta'adda sun kashe sojoji
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu taagerun ƴan ta'adda sun kai hari kan dakarun sojojin Najeriya a jihar Borno da ke yankin Arewa maso Gabas.
Ƴan ta'addan waɗanda ake zargin na ƙungiyar ISWAP ne sun kai harin ne a sansanin sojoji da ke Sabon Birni a ƙaramar hukumar Damboa.
A yayin harin, ƴan ta'adɗan sun kashe sojoji tare da lalata kayan aiki da kwashe makamai masu tarin yawa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng