Rigimar Sarauta: Gwamna Ya Ƙyale Masu Adawa, Ya Miƙa Sandar Mulki ga Sabon Sarki

Rigimar Sarauta: Gwamna Ya Ƙyale Masu Adawa, Ya Miƙa Sandar Mulki ga Sabon Sarki

  • Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya miƙa sandar mulki ga sabon Alaafin na Oyo, Abimbola Akeem Owoade a gidan gwamnati
  • Kwamishinan labarai ya ce zaben sabon Alaafin ya biyo bayan dogon nazari da shawarwari domin tabbatar da ci gaban al’umma
  • Sabon Alaafin ya karɓi sandar mulki bayan shekaru uku da rasuwar tsohon sarki, Oba Lamidi Adeyemi III duk da adawar Oyomesi

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya mika sandar mulki a hukumance ga sabon Alaafin na Oyo, Abimbola Akeem Owoade.

Gwamnan ya miƙa wannan sandar mulkin ne a safiyar Litinin a zauren shugabanni a ofishinsa da ke Ibadan, babban birnin jihar.

Gwamna Makinde ya mika sandar mulki sabon sarkin Ooyo duk da adawar masu nadin sarki
Gwamna Makinde ya kawo karshen rigimar sarauta bayan mika sandar mulki ga Aalafin na Oyo. Hoto: @authorityenigma
Asali: Twitter

Gwamna Makinde ya mika sanda ga sabon sarki

Wannan bikin mika sandar ya gudana ne kusan shekaru uku bayan rasuwar tsohon Alaafin, Lamidi Adeyemi III, inji rahoton Channels TV.

Kara karanta wannan

'Zan kashe waya ta': Gwamna ga masu neman kawo yaransu a ba su kwamishinoni

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Makinde ya mika sandar mulkin duk da takaddamar da aka yi kan zaben sabon Alaafin da gwamnan ya sanar makon da ya gabata.

A ranar Juma’ar da ta gabata, kwamishinan watsa labarai da wayar da kai, Dotun Oyelade, ya ce gwamnan ya amince da nadin Prince Owoade bayan dogon nazari.

Gwamna ya nemi goyon bayan jama'ar Oyo

Ya bayyana cewa sanarwar ta kawo karshen rigingimu na zamantakewa da shari’ar da ake yi tun rasuwar Oba Lamidi Adeyemi a ranar 22 ga Afrilu, 2022.

Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar jihar Oyo da su taya gwamnati murnar wannan nadin tare da ba da goyon baya ga sabon Alaafin.

Gwamnati na ganin wannan nadin zai zama wata babbar dama ta wanzar da zaman lafiya da hadin kai tsakanin al’ummar masarautar Oyo.

Abin da ya jawo takaddamar zaben sarki

Tun da farko, majalisar Oyomesi ko masu zaɓen sarki sun nuna damuwa cewa Gwamna Makinde yana tsoma baki a tsarin zaɓen sabon sarki kuma hakan bai dace ba.

Kara karanta wannan

Aiki ja: Masu nadin sarauta sun taka wa gwamna birki kan nadin sabon sarki

Majalisar Oyomesi ta zaɓi Yarima Lukman Adelodun Gbadegesin a matsayin sabon Alaafin. Amma gwamnan yana da nasa ɗan takarar.

A martaninsa game da zaɓen Yarima Lukman, gwamnan ya nemi masu zaɓen sarautar da su sake fara sabon tsarin zaɓe, inji rahoton BBC.

A cikin wata wasika da ya aika wa masu zaɓen sarki, Makinde, ta hannun Ademola Ojo, ya sanar da su cewa ya naɗa nasa masu zaɓen sarautar wadanda suka zabi Prince Abimbola Akeem Owoade.

Majalisar Oyomesi ta takawa Makinde burki

A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu daga cikin 'yan majalisar Oyomesi sun yi watsi da naɗin Abimbola Owoade a matsayin Alaafin na Oyo.

Masu nadin sarautar sun jaddada goyon bayansu ga Luqman Gbadegesin yayin da suka bayyana cewa tsarin zaben Alaafin ya haramta naɗi ta hanyar son rai.

Gamayyar dattawa sun yi kira ga Gwamna Seyi Makinde da ya janye matakinsa na nadin Abimbola Owoade ko su maka shi kotu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.