Babban Layin Wutar Lantarki Ya Samu Matsala ta Farko a 2025? TCN Ya Yi Bayani

Babban Layin Wutar Lantarki Ya Samu Matsala ta Farko a 2025? TCN Ya Yi Bayani

  • Kamfanin rarraba wuta ya fito ya karyata rahotannin da ake yaɗawa cewa babban layin wuta na ƙasa ya rushe karon farko bayan shiga 2025
  • Mai magana da yawun kamfanin TCN, Ndidi Mbah ya ce rahoton ba gaskiya ba ne, wutar lantarki ya zama

FCT Abuja - Kamfanin rarraba wutar lantarki na Najeriya (TCN) ya karyata rahotannin da ke cewa babban layin wuta ya lalace a ranar Asabar, 11 ga watan Janairu.

Tun farko dai an fara raɗe-raɗin cewa babban layin wuta na ƙasa ya rushe ranar Asabar, lamarin da zai jefa ƴan Najeriya cikin duhu.

Babban layin wuta.
Kamfanin TCN ya musanta raɗe-raɗin cewa babban layin wuta ya lalace Hoto: TCN
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta tattaro cewa rahoton ya yi ikirarin cewa babban layin wutar ya lalace a karo na farko bayan shigowa sabuwar shekara 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kamfanin raba wuta watau TCN ya bayyana cewa rahoton da ake yaɗawa ba gaskiya kuma kuma ba shi da tushe ballantana makama.

Kamfanin TCN ya yi bayanin cewa layin Benin-Omotosho ne ya samu matsala amma ba babban layin wutar lantarki na kasa ba kamar yadda ta jita-jita.

Kara karanta wannan

Abin da ya hana gwamnoni taimakon Malam El Rufai lokacin da aka naɗa shi minista

A cewarsa, matsalar da aka samu a layin Benin-Omotosho ba za ta sa a ɗauke wuta ba, jihar Legas kaɗai matsalar za ta shafa.

Mai magana da yawun TCN, Ndidi Mbah, ya ce rahotannin da ke yawo na katsewar babban layin wuta na ƙasa ba gaskiya ba ne.

“Muna sanar da al'umma cewa babu wata matsala ko faduwar layin wutar lantarki na kasa a yau, sabanin rahotannin karya da ke yawo a kafafen yada labarai,” in ji shi.

Mbah ya ce da misalin karfe 1:41 na rana, layin Osogbo-Ihovour ya samu matsala, wanda ya jawo katsewar layin Benin-Omotosho, amma wannan ya shafi yankin Legas ne kawai.

A cewarsa, kafin matsalar, ana samar da wutar lantarki mai karfin mega 4,335.63 amma bayan katsewar, wutar ta ragu zuwa mega 2,573.23 megawatt.

Wannan a cewar kakakin TCN ya nuna cewa tsarin bai samu wata matsala ta lalacewa gaba daya ba.

Ya ce katsewar ya shafi tashoshin wutar lantarki na Egbin, Olorunsogo, Omotoso, Geregu, da Paras, amma duk an gyara su, sai dai gyaran layin Benin-Omotosho 330kV ne kawai ake kan yi.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta amince da ƙara kuɗin kiran waya da sayen data a Najeriya

Mbah ya yi kira da a guji yada labarai marasa tushe, yana mai cewa: “Dole ne mu fahimci illar da ke tattare da yada bayanan karya da kuma muhimmancin sanar da jama’a gaskiya.”

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262