Lakurawa: Dakarun Sojoji Sun Samu Sabon Umarni kan Masu Tayar da Kayar Baya a Arewa
- Rundunar sojojin Najeriya ta bayar da umarni ga dakarunta kan su yi ƙoƙarin kawo ƙarshen 'yan tada ƙayar bayannan Lakurawa
- Rundunar sojojin ta buƙaci dakarunta da su yi ƙoƙarin ƙarar da ko kuma fatattakar Lakurawan daga Najeriya bakiɗaya
- Kwamandan rundunar haɗin gwiwa na Arewa maso Yamma Oluyinka Soleye ne ya bayar da wannan umarni ga dakarun sojin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - Rundunar sojojin Najeriya ta ba da umarni ga dakarun da ke ƙarƙashin Operation Fansan Yamma kan ƙungiyar ƴan ta'addan Lakurawa.
Rundunar sojojin ta umarci dakarun da su kawar da ƴan ƙungiyar ta’addanci ta Lakurawa ko kuma su fatattake su daga Najeriya gaba ɗaya.
An buƙaci sojojin su kasance masu sadaukarwa
Kwamandan rundunar haɗin gwiwa da ke kula da Arewa maso Yamma, Oluyinka Soleye, ne ya bayar da wannan umarni ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar TheCable.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamandan ya ba da umarnin ne a yayin ziyararsa ga dakarun sojojin da ke Balle, hedkwatar ƙaramar hukumar Gudu a Jihar Sokoto.
Oluyinka Soleye ya yi kira ga sojojin da su kasance masu sadaukarwa ga aikinsu, tare da tabbatar musu da samun cikakken goyon baya daga hedikwatar rundunar sojojin Najeriya.
"Na zo nan ne domin na duba ku kuma na ƙarfafa muku gwiwa kan ƙoƙarinku. Ku sani cewa muna tare da ku."
"Ku yi duk abin da ya dace domin kawar da ƙungiyar Lakurawa ko kuma ku tabbatar da cewa an fatattake su daga yankinmu gaba ɗaya."
- Oluyinka Soleye
Lakurawa sun shafe lokaci mai tsawo
Ya yaba wa dakarun saboda jajircewarsu, tare da tabbatar musu da cewa rundunar sojojin Najeriya za ta ci gaba da bayar da goyon baya don tabbatar da nasarar aikin da suke yi.
A nasa ɓangaren, shugaban ƙaramar hukumar Gudu, Buhari Kurdula, ya yabawa sojojin saboda tabbatar da tsaron yankin.
Buhari Kurdula ya bayyana cewa ƙungiyar ƴan ta'addan Lakurawa ta kasance a yankin tsawon shekara takwas, amma sun kafa sansanin dindindin a cikin shekarar da ta gabata.
Ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan cewa matakan da gwamnati ke ɗauka za su kawo ƙarshen barazanar da ƙungiyar da sauran matsalolin tsaro ke haifarwa.
Wannan umarni ya nuna aniyar gwamnatin Najeriya na kawo ƙarshen ta’addanci da tabbatar da zaman lafiya mai ɗorewa a ƙasar, musamman a yankunan da lamarin ya fi shafa.
Sojojin sun nuna shirinsu na tabbatar da wannan manufa tare da goyon bayan al’umma da sauran masu ruwa da tsaki.
Lakurawa sun halaka 'yan sanda biyu a jihar Kebbi
Wani rahoto da Legit NG ta wallafa a baya ya bayyana yanda wasu 'yan ta'adda da ake zargin 'yan ƙungiyar Lakurawa ne suka halaka jam'ian 'yan sanda biyu a ƙaramar hukumar Argungu da ke jihar Kebbi.
An bayyana cewa 'yan ta'addan sun zo ne a kan babura kuma yawansu ya kai aƙalla 50, sun yi awon gaba da shanu fiye da 200 a kauyen.
Asali: Legit.ng