Hadimin Gwamna Abba Ya Fadi Abin da Zai Faru da Aminu Ado Bayero a karshe
- Hassan Sani Tukur ya na ganin wasu shugabanni a APC ne suke amfani da Aminu Ado Bayero a rikicin masarautar Kano
- Mai ba gwamnan Kano shawarar ya na zargin jam’iyyar APC mai adawa za su bar basaraken yana cizon yatsa ne
- Idan aka gama shari’ar da ake yi game da sarautar Kano, Hadimin na Abba Kabir Yusuf ya ce basaraken zai kunyata ne kawai
- Zuwa yanzu an yi hukunci a kotun daukaka kara wanda bai yi wa lauyoyin Mai martaba Aminu Ado Bayero dadi sosai ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Kano - Hassan Sani Tukur wanda yana cikin mai ba gwamnan jihar Kano shawara ya yi magana game da rikicin masarauta.
Hassan Sani Tukur ya tofa albarkacin bakin nasa ne jim kadan bayan kotun daukaka kara ta yi hukunci a game da dambawar sarautar.
Aminu Ado Bayero da rigimar sarautar Kano
Malam Hassan Sani Tukur ya yi magana a shafin Facebook a jiya, ya na mai yin hasashen makomar Mai martaba Aminu Ado Bayero.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mai taimkawa gwamnan wajen harkokin sadarwa na zamani ya na ganin cewa ‘yan siyasa sun yaudari Sarkin Kano 15, Aminu Ado.
Hassan Tukur ya yi magana a kan yadda dauloli suka rushe a zamunan baya saboda wasu kura-kurai da suka jawo abin kunya.
Aminu Ado bai yi koyi da Muhammadu Sanusi II ba
A rubutun da ya yi, ya ba da misali da yadda Muhammadu Sanusi II ya rungumi kaddara lokacin da gwamnatin Kano ta tsige shi.
Hadimin na Abba Kabir Yusuf yake cewa ba a wulakanta Aminu Ado Bayero kamar yadda aka yi wa Mai martaba Sanusi II a shekarar 2020.
A karshe kuwa Malam Hassan Tukur ya ce sai ga shi ya dawo kan karaga da Abba Yusuf ya zama gwamna ba tare da rasa mutuncinsa ba.
A bara aka tsige Aminu Ado Bayero, da sauran sarakunan Bichi, Rano, Gaya, da Karaye a Kano.
Hassan: "APC ta na amfani da Aminu Ado"
Mai rubutun ya zargi jagororin APC da amfani da basarken kuma hasashensa shi ne nan gaba za su bar Aminu Ado yana cizon yatsa.
Alhaji Hassan yana ganin nan gaba mai martaba zai nemi wadanda suke tunzura shi wajen ganin ya koma gidan Dabo, amma ya rasa su.
Sai dai duk da ya zargi APC da hannu a rikicin, bai iya kama sunan wani ‘dan siyasar Kano ba.
"Ya kamata a gane cewa rashin lissafi da son kan APC suke tunzura Sarkin da aka tsige, abin da bai da ma’ana ga masu hankali.
"Da zai fadawa kan shi gaskiya, zai fahimci babu inda abin zai kai shi kuma sai dai a karshen lamarin a ji kunya.
"Wadanda yake gani a yau, ‘yan siyasan da suke amfani da shi domin maslaharsu, za su watse idan an ci moriyar ganga, su bar shi da takaici."
Kotu ta yi hukunci a rigimar Aminu da Sanusi
Bayan wata da watanni, an ji kotun daukaka ƙara ta dawo da shari'ar rikicin sarauta Kano kamar yadda aka samu labari a ranar Juma'a.
Hukuncin ranar Juma'a ya yi wa gwamnati daɗi domin kuwa an ce kotun tarayya ba ta da hurumi game da abin da ya shafi masarautar jiha.
Asali: Legit.ng