"Za Mu Sauya Zubi," Gwamna Ya Rusa Majalisar Zartarwa, Kwamishinoni Sun Rasa Aiki

"Za Mu Sauya Zubi," Gwamna Ya Rusa Majalisar Zartarwa, Kwamishinoni Sun Rasa Aiki

  • Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya rusa majalisar zartarwa ta jihar a wani mataki na kawo gyara da sababbin dabaru a gwamnatinsa
  • Umo Eno ya ce kwamishinonin sun yi bakin ƙoƙarinsu kuma babu wani daga cikknsu da ya aikata laifin da ya cancanci a kore shi
  • An ruwaito cewa galibin kwamishinonin sun shafe shekaru 10 zuwa sama a ofis tun daga gwamnatin tsohon gwamna, Udom Emmanuel

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Akwa Ibom - A wani mataki na kawo gyara da sababbin dabaru cikin gwamnati, Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya sanar da rushe majalisar zartarwa.

Hakan na nufin mai girma gwamnan ya sallami dukkan kwamishinoninsa daga aiki a jihar da ke kudancin Najeriya.

Gwamna Umo Eno.
Gwamnan Akwa Ibom ya rusa majalisar zartarwa, ya ce zai yi sabon zubi Hoto: Umo Eno
Asali: Twitter

Wannan sanarwa ta zo ne a ranar Juma’a yayin wani zama na bankwana da gwamnan ya yi da kwamishinonin a ɗakin taro na gidan gwamnati a Uyo, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tinubu ta amince da ƙara kuɗin kiran waya da sayen data a Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin gwmana na rusa majalisar zartarwa

Gwamnan ya bayyana cewa matakin ba hukunci ba ne kan wani laifi ko kuskure, sai dai wani yunkuri ne na sabunta gwamnati tare da kawo sababbin ƙwararru cikin tsarin.

Ya jaddada cewa babu wani kwamishina da bai yi aiki yadda ya kamata ba. A cewarsa, dukkan kwamishinonin sun ba da gudunmawa sosai musamman wajen aiwatar da ajendar Arise.

A cewar Fasto Umo Eno, ya rusa majalisar zartarwa ne domin sake kawo sababbin mutane masu gogewa da. za su tallafawa gwamnatinsa ta cika alƙawarin da ta ɗauka.

"Idan dan wani laifi ko rashin aiki, babu kwamishinan da za a kora daga aiki, kowanenku ya yi bakin ƙoƙarinsa musamman kan ajendarmu ta Arise.
"Amma komai ya yi farko zai yi karshe, dole mu rufe wani babin mu buɗe sabo domin kawo ci gaba ga al'umma."

- Umo Eno.

Gwamna Eno zai kawo sababbin hannu

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya gargadi kwamishinoni, ya fadi abin da ba zai lamunta ba

Gwamnan ya bayyana cewa wannan matakin ya zama dole domin tabbatar da ci gaba da gudanar da ayyukan gwamnati cikin nasara.

Ya gode wa kwamishinonin bisa hadin kan da suka bayar tun farkon gwamnatinsa, tare da yi masu fatan alheri a dukkan abin da suka sa a gaba.

Domin nuna godiya da girmamawa, an shirya liyafar bankwana ga ƴan majalisar zartarwa a daren Juma’a a gidan gwamnati.

Yadda gwamna ya gaji kwamishinoni

An bayyana cewa yawancin kwamishinonin sun yi tsawon shekaru goma a ofis, tun lokacin da suka fara aiki a ƙarƙashin tsohon Gwamna Udom Emmanuel.

Wasu daga cikin kwamishinonin tsohon gwamnan sun ci gaba da aiki a ƙarƙashin Gwamna Eno bayan ya sake naɗa su.

Wannan matakin yana nufin gwamnan zai iya sake zaɓar waɗanda za su taimaka wajen cika burinsa na ci gaba da kawo wa jihar cigaba mai ɗorewa.

Hadimin gwamna Eno ya yi murabus

Kara karanta wannan

EFCC: Tsohon gwamna ya shiga matsala, kotu ta ƙwace masa sama da N200m

A wani labarin, an ji cewa mai taimakawa gwmanan Akwa Ibom kan harkokin wayar da kan jama'a, Aniekeme Finbarr ya yi murabus daga muƙaminsa.

Hadimin gwamnan ya ajiye aiki ne bayan shafe shekaru 10 yana aiki tun daga gwamnatin Udom Emmanuel.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262