Gwamna Ya Kawo Karshen Rigimar Sarauta Ta Shekaru 2, Ya Amince da Nada sabon Sarki

Gwamna Ya Kawo Karshen Rigimar Sarauta Ta Shekaru 2, Ya Amince da Nada sabon Sarki

  • Gwamna Seyi Makinde ya amince da nadin Yarima Abimbola Owoade a matsayin sabon Alaafin na Oyo, bayan zurfafa bincike
  • Sabon nadin ya kawo karshen rikicin siyasar da ya barke tun bayan rasuwar tsohon Alaafin, Oba Lamidi Adeyemi III a 2022
  • To sai dai kuma, masu nadin sarki sun yi watsi da umarnin Makinde, suna ikirarin cewa an riga an zabi Yarima Lukman Gbadegesin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Oyo - Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya amince da nadin Yarima Abimbola Owoade a matsayin sabon Alaafin na Oyo.

Sanarwar nadin Owoade ta fito ne ranar Juma’a daga kwamishinan labarai da wayar da kan jama’a na jihar, Dotun Oyelade.

Gwamna Seyi Makinde ya yi magana yayin ya amince da nadin sabon sarki
Gwamna ya nada sabon sarkin Oyo yayin da masu nadin sarauta suka bijire masa. Hoto: @seyiamakinde
Asali: Twitter

Gwamna Makinde ya nada sabon sarki a Oyo

Sanarwar ta ce an zabi Yarima Owoade ne bayan tuntuba mai zurfi da binciken al’ada da majalisar sarakuna ta Oyomesi ta gudanar, inji rahoton Punch.

Kara karanta wannan

Aiki ja: Masu nadin sarauta sun taka wa gwamna birki kan nadin sabon sarki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Gwamna Makinde ya amince da nadinYarima Abimbola Akeem Owoade, bayan tuntuba da binciken al’ada tare da daukar shawarar majalisar Oyomesi."

Kwamishinan harkokin kananan hukumomi da sarauta, Ademola Ojo, ya ce wannan sanarwa ta kawo karshen rigingimu na doka da zamantakewa bayan rasuwar Alaafin.

Gwamna ya nemi hadin kan al'ummar Oyo

Sanarwar ta ci gaba da cewa:

“Wannan matakin ya kawo karshen rikicin doka da ya biyo bayan rasuwar tsohon Alaafin, Oba Lamidi Adeyemi III, wanda ya rasu a 22 ga Afrilu, 2022.”

Kwamishinan ya bukaci mutanen jihar Oyo da su goyi bayan sabon sarkin tare da taya gwamnati da jama'a murnar ganin wannan lokaci mai muhimmanci.

Sanarwar ta ce gwamnan jihar na da yakinin cewa mulkin sabon Alaafin zai kawo zaman lafiya, hadin kai, da ci gaba ga masarautar Oyo.

"Mulkinsa zai kawo ci gaban Oyo" - Gwamna

Sanarwar ta kara da cewa:

“Muna addu’ar zamaninsa ya kawo ci gaba da zaman lafiya ga mutanen Oyo tare da karfafa tarihin gadon masarautar Alaafin."

Kara karanta wannan

An shiga jimami da tsohon shugaban Majalisar Dokoki ya yi babban rashi

An bukaci al’ummar jihar Oyo da su marawa sabon sarki baya a matsayin shugabansu na masarauta mai tarihi.

Bayan rasuwar tsohon Alaafin, Oba Lamidi Adeyemi III, tsarin zabin sabon sarki ya haifar da cece-kuce.

Masu nadin sarki sun bijirewa gwamna

A kwanan nan ne Gwamna Makinde ya umarci a gudanar da sabon tsarin zaben, amma masu nadin sarauta biyar suka yi watsi da wannan umarni a ranar Alhamis.

Masu nadin sarautar sun hada da Basorun na Oyo, Yusuf Akinade; Lagunna, Wakeel Akindele; Akinniku, Hamzat Yusuf; da wasu masu sarauta masu wakilci.

Sun yi ikirarin cewa Yarima Lukman Gbadegesin shi ne Alaafin da aka riga aka zaba, suna kuma nuna hujja da shari’ar da ke gudana.

Lauyan masu nadin sarauta, Adekunle Sobaloju, ya bayyana matakin gwamnan na nada sabon sarki a matsayin rashin bin doka.

Gwamna Makinde ya yi sauye sauye

A wani labarin, mun ruwaito cewa Gwamna Seyi Makinde ya yi garambawul a majalisar zartarwar jihar Oyo, ya sauya wa wasu kwamishinoni wurin aiki.

Mun rahoto Makinde ya canja kwamishinonin ma'aikatar kananan hukumomi da masarautun Oyo, da wasu ma'aikatu a gwamnatinsa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.