Kungiyoyin Arewa Sun Sake Bijerewa Kudirin Haraji, Sun Fadi Illarsa ga Talaka
- Gamayyar kungiyoyin farar hula na Arewacin Najeriya ta mika bukata ga ‘yan majalisar dokoki na yankin Arewa a kan kudirin haraji
- Matasan sun yi taro a Abuja domin nuna rashin amincewa da kudirin harajin da aka gabatar, suna ganin ba ya dace 'yan kasa ba
- Kungiyoyin Arewa sun bayyana cewa kudirin harajin na iya kara haɓaka talauci, rage ayyukan masana'antu da kara jawo wahala
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna - Gamayyar kungiyoyin farar hula na Arewacin Najeriya Hadakar Kungiyoyin Arewa (CNG, sun mika bukata ga ‘yan majalisar dokoki daga yankin Arewa a kan kudirin haraji.
A wata sanarwa da suka fitar bayan taron da suka gudanar a ranar Alhamis a Arewa House, Kaduna, kungiyoyin sun bayyana cewa kudirin harajin bai dace da halin da ake ciki a kasar ba.
Arise News ta ruwaito cewa Muhammed Sanusi Ali ne ya rattaba hannu kan sanarwar a madadin kungiyoyin sun bukaci ‘yan majalisun yankin su yi watsi da batun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiyoyin Arewa sun yi gargadi
Daily Post ta wallafa cewa kungiyoyin sun bayyana cewa tsarin harajin na iya kara talauci, rashin aikin yi, durkusar da cibiyoyin ilimi, da kuma tabarbarewar matsalolin tattalin arziki.
Sanarwar ta kara da cewa:
"A taron, an cimma matsaya kan wasu muhimman abubuwa dangane da kudirin harajin da aka gabatar. Wanda suka halarci taron sun lura cewa kudirin harajin ba zai zama hanyar bunkasa tattalin arziki ba, illa kara dagula matsalolin tattalin arziki da ke addabar Arewa da Najeriya baki daya."
Kungiyoyin Arewa sun fadi illar kudiri haraji
Sanarwar ta ce bayan tsananta talauci, kudirin harajin zai durkusar da kananan masana’antu da dama da tuni suke fama da matsalolin tattalin arziki a yanzu.
Haka nan, kungiyoyin sun nuna damuwa kan wasu sassa na kudirin da ke nuni da rage kudaden da ake bai wa manyan cibiyoyi na kasa kamar su TETFUND, NITDA, da NASENI.
‘A janye kudirin haraji,” Kungiyoyin Arewa
Gamayyar kungiyoyin Arewa ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta janye kudirin harajin nan take, tare da daukar matakin da zai dace da bukatun jama’a na warware talauci.
Sanarwar gamayyar ta bukaci shugabanni su mayar da hankali wajen samar da hanyoyin da za su rage radadin matsalolin tattalin arziki a kasar maimakon kara dagula lamarin.
Kotu nemi bayani a kan kudirin haraji
A wani labarin, mun ruwaito cewa Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta umarci Ministocin Gida da na Shari'a su bayyana gabansu a cikin kwanaki uku kan tsarin harajin kasashen waje.
Mai shari'a Inyang Ekwo ne ya bayar da wannan umarnin bayan da lauyan kungiyar New Kosol Welfare Initiative ya shigar da korafi a kotun, ana neman dakatar da aiwatar da tsarin harajin.
Kudurin harajin gwamnatin Najeriya, karkashin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ya ki samun karbuwa a tsakanin talakawa da wasu daga cikin masu abin hannunsu a fadin Najeriya.
Asali: Legit.ng