Yan Bindiga Sun Bi Kauyuka Suna Yanka Mutane da Wuka, Sun Kashe Rayuka
- ‘Yan bindiga sun kai hare-hare a wasu kauyuka a karamar hukumar Orsu ta jihar Imo, inda suka kashe mutum 18
- Rundunar ‘yan sandan jihar ta ce an kafa tawaga domin gano musabbabin harin da kuma hukunta masu laifi
- Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne a yayin da ake bukukuwan wasu gargajiya da ake gudanarwa a yankin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Imo - ‘Yan bindiga sun kai hari mai muni a wasu kauyuka a Karamar Hukumar Orsu ta Jihar Imo, suka kashe mutane 18 a hare-haren da suka gudana a rana ɗaya.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne ranar Lahadi, 5 ga Janairu, 2025, a kauyukan Umukabia, Eziawa, Ihittenasa, Umuhu, Amaoku, da Amaebe, duk a cikin yankin Orsu.
Punch ta wallafa cewa rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar mummunan harin tare da bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike domin gano musabbabin harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka kai hari a jihar Imo
Bayanan da aka tattara sun nuna cewa maharan sun kai harin ne a lokacin da ake gudanar da wani bikin gargajiya a yankin.
Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa bayan kammala bikin, wasu mazauna yankin da suka dawo daga kasashen waje domin bikin Kirsimeti sun je wani shagon shan shayi.
The Cable ta wallafa cewa sai daga baya, mutane sun gano dukkan mutanen da ke cikin shagon kwance a cikin jini, tare da raunuka masu muni na wukake a jikinsu.
Shaidar gani da idon ya ce,
“Mutane tara ne aka kashe a shagon, kuma babu wanda ya ji sautin harbin bindiga ko gardama a lokacin.
Muna zargin cewa harin ya samu hadin kan wasu daga cikin mutanen yankin da ke aiki tare da ‘yan kungiyar IPOB da ESN.”
Adadin wadanda aka kashe yayin harin
Rahotanni sun bayyana cewa an gano gawa tara a shagon shan shayi, sai kuma wasu mutane uku 'yan gida daya a kauyen Umukabia.
Haka zalika, an gano gawar mutane biyar a kauyen Eziawa da kuma wasu biyar daga Ihittenasa, dukkaninsu da raunukan gatari a jikinsu.
Shaidar gani da idon ya kara da cewa,
“Abin mamaki ne yadda waɗannan hare-haren suka faru ba tare da wani ya gani ba. Mun rasa mutane 18 a rana ɗaya.”
Martanin hukumomi a jihar Imo
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, DSP Henry Okoye, ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce CP Aboki Danjuma, ya umarci a gano wadanda ke da hannu a harin.
Kwamishinan ya yi kira ga mazauna yankin da su kwantar da hankulansu tare da bayar da haɗin kai wajen binciken da ake gudanarwa.
Wani jami’in ‘yan sanda da ya nemi a ɓoye sunansa ya bayyana cewa maharan na kokarin tsoratar da mazauna yankin ne domin su bar gidajensu.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ake kokarin kawo zaman lafiya a Orsu bayan kwato garin a hannun kungiyar IPOB da ESN da suka shafe shekaru hudu suna cin karensu ba babbaka.
'Yan sanda sun kwato makamai a Benue
A wani rahoton, kun ji cewa 'yan sanda sun kwato makamai a wani gagarumin samame da suka kai kan 'yan ta'adda a jihohi.
Rundunar 'yan sanda ta bayyana cewa ta kwato makamai a jihar Benue bayan kai farmaki wata maboyar 'yan bindiga masu garkuwa da mutane.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng