Rikicin Kungiyoyin Asiri Ya Jawo Asarar Rayukan Mutum 3
- An shiga jimami a jihar Bayelsa bayan wasu matasa ɗauke da makamai sun hallaka mutum uku har gidan barzahu
- Matasan waɗanda ake zargin ƴan ƙungiyar asiri ne sun kai harin ne a ƙauyen Igbogene da ke ƙaramar hukumar Yenagoa
- Rundunar ƴan sandan jihar ta tabbatar da aukuwar lamarin wanda ya jefa mutanen ƙauyen cikin firgici a halin yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bayelsa - Wasu matasa ɗauke da makamai da ake zargin mambobin ƙungiyar asiri ta Greenlanders ne, sun kai mummunan hari a jihar Bayelsa.
Ƴan ƙungiyar asirin sun kai harin ne a ƙauyen Igbogene da ke ƙaramar hukumar Yenagoa a jihar Bayelsa, da misalin ƙarfe 8:00 na daren ranar Laraba.
Jaridar Leadership ta rahoto cewa maharan waɗanda yawansu ya kai mutum 10, sun hallaka mutum uku yayin harin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ƴan ƙungiyar asiri sun yi ta'asa a Bayelsa
Daga cikin mutanen da suka kashe har da ɗan tsohon shugaban ƙungiyar ƴan sa-kai, wanda aka fi sani da "Money Sweet", rahoton jaridar Daily Trust ya tabbatar da batun.
Harin ya jefa mazauna yankin cikin tsoro, inda suka riƙa guduwa tare da kulle ƙofofinsu domin tsira daga miyagun.
Lamarin ya bar al’ummar ƙauyen cikin jimami da tashin hankali saboda rashin tsaro da ke ƙara ƙamari a yankin.
Wani mazaunin yankin ya bayyana cewa wanda aka fara kashewa a harin shi ne ɗan tsohon shugaban ƙungiyar ƴan sa-kan, wanda aka harbe a kusa da gidansa.
Mutum na biyu da aka kashe ba mamba ba ne na wata ƙungiyar asiri, amma tsautsayi ya faɗa kansa ne bayan ya ƙi bayyana inda ɗan uwansa yake.
Me ya jawo aka kai harin?
Bincike ya nuna cewa harin ya samo asali ne daga rikicin ƙungiyoyin asiri guda biyu da ake yi wa laƙabi da Bobos da Greenlanders.
Rahoton ƴan sanda ya tabbatar da mutuwar mutane uku a harin, amma mazauna yankin sun ce mutum biyu ne suka mutu, yayin da na uku ke kwance a asibiti saboda raunin harbin bindiga.
Shugaban matasan ƙauyen Igbogene, Ezekiel Igbenivie, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce waɗanda suka kai harin sun tsere.
"Amma ɗaya daga cikin waɗanda aka harba yana raye, kuma yana karɓar magani."
- Ezekiel Igbenivie
Me ƴan sanda suka ce kan lamarin?
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar Bayelsa, Musa Mohammed, ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa waɗanda aka harba sun haɗa da Donaldson Mison mai shekara 28, Addy Mulan mai shekara 27, da Greenboy Dudella mai shekara 29.
Jami'an tsaro sun daƙile harin ƴan bindiga
A wani labarin kuma, kun ji cewa jami'an na haɗin gwiwa sun samu nasarar daƙile wani hari da ƴan bindiga suka kai a jihar Sokoto da ke yankin Arewacin Najeriya.
Jami'an da suka haɗa da ƴan sanda da na rundunar tsaron Sokoto, sun yi nasarar kuɓutar da fasinjojin da aka sace bayan sun yi musayar wuta da ƴan bindigan.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng