Gwamnatin Tinubu Ta Amince da Ƙara Kuɗin Kiran Waya da Sayen Data a Najeriya

Gwamnatin Tinubu Ta Amince da Ƙara Kuɗin Kiran Waya da Sayen Data a Najeriya

  • Ministan sadarwa na Najeriya, Bosun Tijani ya ce nan ba da jimawa ba za a yi karin kudin kira, tura saƙo da sayen data a ƙasar nan
  • Tijani ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ta amince kamfanonin su kara kudin ayyukansu amma ba zai kai ƙarin kaso 100% ba
  • Ya ce manufar gwamnati shi ne a samu ingantaccen sabis na sadarwa ba tare da tangarɗa ba domin amfanin al'umma

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ministan sadarwa, ƙirkire-ƙirkire, da tattalin arzikin zamani, Dakta Bosun Tijani, ya bayyana cewa za a yi karin kudin kira, tura sako da kudin sayen data nan ba da dadewa ba.

Amma ministan ya tabbatarwa ƴan Najeriya cewa karin ba zai kai kaso 100 cikin 100 ba kamar yadda wasu kamfanonin sadarwar suka nema.

Kara karanta wannan

Ministan Tinubu ya sa labule da MTN, Airtel da wasu kamfanonin sadarwa, bayanai sun fito

Ministan sadarwa, Bosun Tijani.
Gwamnatin Tinubu ta Amince da karin kudin kiran waya da sayen data a Najeriya Hoto: @bosuntijani
Asali: Twitter

Dakta Tijani ya yi wannan bayani ne bayan wani taron tattaunawa da kamfanonin sadarwa (MNOs) a Abuja a ranar Laraba, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce ana ci gaba da yin shawarwari tare da masu ruwa da tsaki domin cimma matsaya kan batun ƙarin kafin sanar da al'umma.

Gwamnatin Tinubu ta ƙi yarda da ƙarin 100%

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya (NAN) ya ruwaito cewa kamfanonin sadarwa kamar MTN, Airtel, Glo da sauransu sun buƙaci a amince su kara kuɗin da kaso 100%.

Sai dai ministan ya tabbatar da cewa gwamnatin tarayya ba za ta amince da wannan bukata ba gaba daya.

“Kun ga ni a makonnin da suka gabata cewa wadannan kamfanoni sun matsa a ba su dama su ƙara kuɗin sadarwa. Sun bukaci karin kaso 100%, amma ba za mu amince da hakan ba,” in ji Tijani.

Yaushe kamfanonin sadarwa za su yi ƙarin?

Kara karanta wannan

'Magana ta fara fitowa': Hamza Al Mustapha ya fadi dalilin ganawa da El Rufa'i

Ya kara da cewa hukumar sadarwa ta Najeriya (NCC) za ta fitar da umarni nan ba da dadewa ba kan yadda za a gudanar da karin kudin kira, data da saƙo.

Bosun Tijani ya ce NCC za ta fitar karin da za a yi cikin adalci, tare da kare masu amfani da layukan sadarwa daga tsadar da ba za su iya dauka ba.

“Gwamnati tana kokarin samar da daidaito a tsakanin masu amfani da sabis da kuma kamfanonin sadarwa, ta yadda za a kare hakkin jama’a kuma a tabbatar kamfanonin za su iya ci gaba da zuba jari mai tsoka,” in ji shi.

Gwamnatin Tinubu za ta gyara fannin sadarwa

Ministan ya jaddada cewa akwai bukatar samar da ingantattun dokoki don bunkasa bangaren sadarwa a Najeriya.

“A baya mun bar zuba jarin a hannun masu zaman kansu, wanda yawanci suna mayar da hankali ne ga wuraren da za su samu riba cikin kankanin lokaci. Amma yanzu, gwamnati tana son yin gyare-gyare."

Kara karanta wannan

Gwamnatin Sokoto ta fadi abin da za ta yi wa wadanda gobarar kasuwar Kara ta shafa

Ya kuma bayyana cewa manufar gwamnati ba wai karin kuɗin ba ne, amma ta fi maida hankali kan samar da ingantacciyar sadarwa da wadatar sabis domin amfanin jama’a.

Ministan Tinubu ya gana da kamfanonin sadarwa

A wani labarin kun ji cewa ministan sadarwa. Bosun Tijani ya gana da wakilan kamfanonin MTN, Airtel da sauransu kan bukatar ƙarin kudin sadarwa.

Hukumomin gwamnatin Najeriya masu ruwa da tsaki a harkokin sadarwa sun halarci zaman na ranar Laraba, 8 ga watan Janairu, 2025.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262