Kwana Ya Kare: Bayan Halartar Taro da Gwamna, Kwamishina Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

Kwana Ya Kare: Bayan Halartar Taro da Gwamna, Kwamishina Ya Riga Mu Gidan Gaskiya

  • Kwamishinan harkokin yawon buɗe idanu, al'adu da fasaha na jihar Kuros Riba, Abubakar Ewa ya rasu ranar Laraba, 8 ga watan Janairu, 2025
  • Rasuwar dai ta girgiza al'ummar jihar Kuros Ribas kasancewar marigayin ya halarci taron majalisar zartarwa wanda Gwamna Otu ya jagoranta a ranar
  • An ruwaito cewa galibin abokan aikinsa a gwamnatin Kuros Riba sun je asibitin da ya rasu domin yi wa ƴan uwa da abokan arziki ta'aziyya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Cross River - Kwamishinan harkokin yawon buɗe ido, fasaha, da al’adu na jihar Kuros Riba, Mista Abubakar Robert Ewa, ya riga mu gidan gaskiya.

Ewa ya rasu da yammacin ranar Laraba a Asibitin Kwararru na Arubah da ke Kalaba, babban birnin jihar Kuros Riba da ke Kudu maso Kudancin Najeriya.

Abubakar Robert Ewa.
Kwamishina a Kuros Riba, Abubakar Robert Ewa ya rasu Hoto: Calabar Gist
Asali: Facebook

Channels tv ta ce har zuwa lokacin haɗa wannan rahoton, ƴan majalisar zartarwa na jihar Kuros Riba da sauran hadiman Gwamna Bassey Otu suna asibitin Arubah.

Kara karanta wannan

Gwamna Abba ya gargadi kwamishinoni, ya fadi abin da ba zai lamunta ba

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tattaro cewa kwamishinoni da hadimin gwamnan sun hallara a asibitin domin alhinin wannan rashi da kuma yi wa iyalan marigayin ta'aziyya.

Kwamashina ya rasu bayan ganawa da gwamna

Bayanai sun nuna cewa marigayi kwamishinan ya halarci taron majalisar zartarwa na jihar wanda Gwamna Otu ya jagoranta tun da sanyin safiyar Laraba.

Amma kuma bayan taron, Allah ya yi masa rasuwa a wannan rana ta Laraba, 8 ga watan Janairu, 2025, sai dai ba a bayyana abin da ya yi ajalinsa ba kawo yanzu.

Mukaman da marigayi kwamishinan ya riƙe

Marigayi Abubakar Robert Ewa ya taba rike mukamin sakatare, sannan daga bisani ya zama shugaban ƙaramar hukumar Boki a Kuros Ribas.

Haka kuma, ya taba zama mai bai wa gwamna shawara na musamman kan harkokin all’umma da kuma sakatare na kwamitin yaki da sare itatuwa ba bisa ka’ida ba.

Rasuwar ta zo wa mutane da dama a jihar Kuros Riba a matsayin abin mamaki, kasancewar Ewa ya halarci taron majalisar zartarwa na jihar da safe a ranar Laraba, rahoton Daily Trust.

Kara karanta wannan

Najeriya ta ƙara yin babban rashi, Allah ya yi wa tsohon kwamishina rasuwa

Al'ummar Kuros Ribas sun shiga alhini

Marigayi Abubakar Robert Ewa ya shafe shekaru masu yawa yana hidima ga al’ummar jihar Kuros Riba a muƙamai daban daban da ya riƙe a rayuwarsa.

Lokaci na karshe da mamacin ya fito bainar jama'a shi ne a taron al'ada na Arts and Crafts na cibiyar Al'adu a Calabar, inda ya sanar da shirin gwamnati na sabunta cibiyar.

Rasuwar Abubakar Ewa babban rashi ne ga jihar Kuros Riba musamman a bangaren harkokin yawon buɗe idanu da al’adu, wanda ya yi aiki tukuru wajen bunkasawa.

Tsohon kwamishina a Benuwai ya mutu

A wani labarin, mun kawo maku cewa tsohon kwamishinan ayyuka na jihar Benuwai kuma ɗan uwan sojan da ya yi yunƙurin juyin mulki a 1990, Farfesa Joseph Orkar ya rasu.

Gwamna Hyacinth Alia ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da abokan arziki, inda ya bayyana mamacin a matsayin wanda ya gina al'umma.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262