Dara Ta Ci Gida: Hukumar EFCC Ta Tsare Wasu Jami'anta, Ta Fadi Dalili
- Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta tsare wasu daga cikin jami'anta
- EFCC ta tsare jami'an ne guda 10 da ke aiki a ofishinta na Legas bayan an nemi wasu kayayyakin aikin hukumar da ke hannunsu an rasa
- Shugaban hukumar EFCC ne ya ba da umarnin cafkewa tare da tsare jami'an har sai an kammala gudanar da bincike kan zargin da ake yi musu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC) ta tsare wasu daga cikin jami'anta.
Hukumar EFCC ta tsare jami'an ne guda 10 da ke aiki a ofishinta na Legas, bisa zargin satar kayan aiki.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da hukumar EFCC ta sanya a shafinta na X, a ranar Laraba, 8 ga watan Janairun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa aka tsare jami'an hukumar EFCC
A cewar hukumar, tsare jami'an da aka yi na daga cikin binciken cikin gida da ake gudanarwa domin tabbatar da gaskiya da riƙon amana a tsakanin ma’aikatan EFCC.
Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya bayar da umarnin kamawa tare da tsare jami’an, a wani yunƙuri na magance ɗabi’un cin hanci da rashin da’a a tsakanin ma’aikatan hukumar.
A halin yanzu, jami’an na EFCC da aka tsare suna fuskantar tambayoyi kan gazawarsu wajen bayar da cikakken bayani kan wasu kayayyakin aiki da suka ɓace a hannunsu.
"Jami’an da aka kama a makon da ya gabata bisa umarnin shugaban hukumar, Mista Ola Olukoyede, suna amsa tambayoyi kan satar wasu kayayyakin aiki da suka kasa bayar da bayanin inda suke."
"Masu bincike suna samun gagarumar nasara, kuma duk wanda aka samu da laifi zai fuskanci tsauraran matakan ladabtarwa."
- Hukumar EFCC
EFCC ta kori jami'ai
A ranar Litinin, hukumar EFCC ta sallami jami’anta 27 saboda aikata ayyukan zamba da kuma rashin ɗa’a.
An dauki wannan mataki ne bisa shawarar da kwamitin ladabtar da ma’aikatan hukumar EFCC ya ba da.
Karanta wasu labaran kan EFCC
- Yadda hukumar EFCC ta yi farautar manyan 'yan siyasar Najeriya a shekarar 2024
- EFCC ta gano wani mai daukar nauyin ta'addanci, kotu ta garkame asusun bankuna 24
- EFCC: Wasu ma'aikatan gwamnatin tarayya sun shiga matsala, an kore su daga aiki
Hukumar EFCC ta ƙwato N248bn
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa da yi wa tattalin arziƙin ƙasa zagon ƙasa (EFCC), ta samu nasarar makuɗan kuɗaɗe a shekarar 2024.
Ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro (ONSA) ne ya bayyana nasararorin da hukumar yaƙi da cin hancin ta samu.
Ofishin na ONSA ya bayyana cewa hukumar EFCC ta ƙwato kuɗi Naira biliyan 248, Dala miliyan 105 da kuma gidaje 753 daga hannun masu halin ɓera.
Asali: Legit.ng