Gwamna Abba Ya Gargadi Kwamishinoni, Ya Fadi Abin da ba Zai Lamunta ba
- Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya sanar da ƴan majalisar zartarwar jihar.abin da ba zai yarda da shi ba a gwamnatinsa
- Abba Kabir Yusuf ya bayyanawa kwamishinoninsa cewa ba zai lamunci rashin biyayya da duk wani abu da zai kawo rarrabuwar kawuna a majalisar zartarwar
- Gwamnan ya yi maraba da sababbin kwamishinonin da aka rantsar, inda ya buƙace su da su jajirce wajen sauke nauyin da aka ɗora musu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aika da saƙo ga ƴan majalisar zartarwar jihar.
Gwamna Abba ya buƙaci mambobin majalisar zartarwa ta jihar Kano da su kaucewa kowane irin abu da za zai janyo rashin biyayya da rarrabuwar kawuna a cikin gwamnatinsa.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya a shafinsa na Facebook.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya ja kunnen kwamishinoni
Gwamnan ya tunatar da kwamishinonin muhimmancin biyayya, gaskiya, da girmama juna a cikin majalisar, yana mai cewa za a ɗauki ƙwaƙƙwaran mataki kan duk wanda aka samu ya saɓa ka’idojin da aka gindaya.
Ya bayyana hakan ne yayin bude taron majalisar zartarwa karo na 23 da aka gudanar a dakin taro na majalisar da ke fadar gwamnati.
Gwamnan ya tarbi sababbin kwamishinonin da aka rantsar zuwa majalisar zartarwar, inda ya jaddada mahimmancin gaskiya, nuna ƙwarewa, da yin aiki tare domin samun nasara.
Wace shawara Gwamna Abba ya ba da?
“Mun samu damar rantsar da sababbin kwamishinoni bayan majalisar dokokin jihar Kano ta yi nasarar tantancesu."
“Ana umartar waɗanda suka samu muƙaman da su jajirce wajen sauke nauyin da aka ɗora musu, kuma a madadin majalisa, ina sake taya murna ga sababbin kwamishinonin."
“Ina son jaddada cewa ba ma tsammanin komai face gaskiya, jajircewa, da tsantsar himma daga kowane daga cikinku. Ina kuma kira gare ku da ku ba da cikakken haɗin kai da dukkanin mambobin majalisar."
“Ba ma buƙatar rashin gaskiya, rikici, ko banbance-banbance marasa amfani daga kowannenku. Duk wanda ya yi kokarin kawo rarrabuwar kai zai gamu da hukunci. Yanzu sabon lokaci ne."
- Gwamna Abba Kabir Yusuf
Gwamnan Kano ya faɗi nasarorin da ya samu
Gwamnan ya yi wa majalisar bayanin ayyukan gwamnatinsa a cikin watanni uku na ƙarshen shekarar 2024, inda ya nuna farin ciki bisa nasarorin da aka cimmawa.
A cikin rahoton, gwamnan ya bayyana dawowar ɗalibai 150 cikin nasara daga jami’o’in ƙasar Indiya bayan kammala karatun digiri na biyu.
Gwamna Abba zai raba N3bn
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Kano, Abba Kabor Yusuf, ya waiwayo kan mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a sassan daban-daban na jihar.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya kammala shirye-shirye raba maƙudan kuɗaɗen sa suka kai N3bn ga mutanen da ambaliyar ruwa ta ritsa da su a lokacin daminar da ta wuce.
Abba Kabir Yusuf ya ce tuni aka tantance mutanen da za su amfani da rabon da kuma adadin kuɗin da kowannensu zai samu.
Asali: Legit.ng