Gwamna Abba Zai Rabawa Mutane Kano Naira Biliyan 3, Ya Faɗi Waɗanda Suka Cancanta

Gwamna Abba Zai Rabawa Mutane Kano Naira Biliyan 3, Ya Faɗi Waɗanda Suka Cancanta

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya ce gwamnatinsa ta kammala shirin rabawa waɗanda ambaliya ta shafa a jihar Kano tallafin Naira biliyan 3
  • A wata sanarwa da mai magana da yawun Abba ya fitar, gwamnan ya ce gwamnatin tarayya ce ta turo kuɗin a watannin da suka gabata
  • Gwamna ya kafa kwamitocin da za su sa ido kuma su tabbatar da kuɗaɗen sun isa hannun waɗanda suka dace a kananan hukumomi 44

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya kammala shirye-shiryen raba Naira biliyan 3 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a kwanakin baya a fadin jihar.

Abba Gida-Gida ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a wurin taron majalisar zartarwa ta jihar karo na 23 da aka gudanar a fadar gwamnatin Kano.

Gwamna Abba Kabir.
Gwamnan Kano zai sauke nauyin raba tallafin N3bn ga waɗanda ambaliya ta shafa Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Mai magana da yawun gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar, jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

EFCC: Tsohon gwamna ya shiga matsala, kotu ta ƙwace masa sama da N200m

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Idan baku manta ba gwamnatin tarayya ta ba kowace jiha Naira biliyan 3 da birnin tarayya Abuja a matsayin tallafin rafe raɗaɗin ambaliyar ruwa.

Gwamnatin ta ba jihohi waɗannan kuɗaɗen ne bayan mummunar ambaliyar da ta afku a jihar Borno, da wasu da suka afku a jihohi da dama ciƙi har da Kano.

Gwamna Abba zai rabawa mutane N3bn

Gwamna Abba Yusuf ya bayyana cewa tuni aka turo kudin kuma gwamnatinsa ta adana su a baitul-malin Kano.

A cewarsa, an yi haka ne domin ba da dama da isasshen lokacin tantance wadanda abaliyar ta shafa kuma suka cancanta a ba su tallafin kudin kafin a fara rabon.

Abba ya ce hakan zai taimaka wajen kaucewa almundahana yayin rabon tallafin ga waɗanda wannan ibtila'i ya shafa a wasu sassan kananan hukumomin Kano.

Gwamnan Kano ya ce:

“Yanzu da mun kammala shiri, muna da cikakken jerin sunayen wadanda suka cancanta da kuma adadin kudin da kowannensu ya cancanta ya karba. Za mu fara rabon nan ba da jimawa ba."

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano ya gwangwaje wata hadimarsa da kyautar gidan N19m, ta karbi mabudi

Gwamnan Kano ya kafa kwamitocin sa ido

Abba Kabir ya kuma sanar da kafa kwamitoci daban-daban da za su kula da rabon kudaden a kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Ya ce an kafa waɗannan kwamitoci ne domin su sa iso sannan su tabbatar da cewa kudaden sun isa hannun wadanda suka dace.

“Mun ajiye kudaden ne don tabbatar da cewa an yi amfani da su wajen rage wahalhalun wadanda ambaliyar ruwa ta shafa kai tsaye."
Mun himmatu wajen tabbatar da gaskiya, adalci, da kulawa da bukatun jama’a," in ji shi.

Gwamna Abba ya ba hadimarsa kyautar gida

A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya gwangwaje wata hadimarsa da kyautar gida da ya kai datajar Naira miliyan 19.

Gwamnan ya ba mai taimaka masa kan harkokin mata, Hajiya Hauwa Muhammad kyautar gidan ne saboda gudummiwar da take bayarwa wajen ci gaban Kano.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262