Ministan Tinubu Ya Sa Labule da MTN, Airtel da Wasu Kamfanonin Sadarwa, Bayanai Sun Fito

Ministan Tinubu Ya Sa Labule da MTN, Airtel da Wasu Kamfanonin Sadarwa, Bayanai Sun Fito

  • Ministan sadarwa na Najeriya, Bosun Tijani ya shiga taro da wakilan MTN, Airtel da sauran kamfanonin sadarwa da ke aiki a ƙasar nan
  • Wannan zama dai na zuwa ne a daidai lokacin da kamfanonin suka buƙaci gwamnatin tarayya ta amince su nunka kudin sadarwa kamar kira, sako da data
  • Ana sa ran wannan taron zai tattauna kan wannan batu na karin kudin kira da na data wanda ke taka muhimmiyar rawa a rayuwar ƴan Najeriya ta yau da kullum

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ministan sadarwa, kirkire-kirkire da tattalin arzikin zamani, Bosun Tijjani ya shiga ganawa yanzu haka da wakilan kamfanonin sadarwa a birnin Abuja.

An tattaro cewa taron zai tattauna ne kan matsin lambar da kamfanonin sadarwa ke yi na kara kudin kira, tes da data saboda tsadar kayayyakin da ake fama da ita.

Kara karanta wannan

EFCC: Tsohon gwamna ya shiga matsala, kotu ta ƙwace masa sama da N200m

Ministan sadarwa, Bosun Tijani.
Ministan sadarwa ya shiga ganawa da wakilan MTN da sauran kamfanonin sadarwa Hoto: @Imranmuhdz
Asali: Twitter

Minista ya shiga zama da MTN, Airtel da Glo

Jaridar The Nation ta gano cewa wakilan manyan kamfanonin sadarwa irin su MTN Nigeria, Airtel, Globacom, 9Mobile, da sauransu sun halarci wannan taro.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Taron wanda aka fara yau Laraba, 8 ga watan Janairu, 2025 da safe ya samu halartar hukumomin gwamnati masu ruwa da tsaki kan harkokin sadarwa.

Daga cikin hukumomin gwamnatin tarayya da aka hanga a wurin taron har da hukumar kula da harkonin sadarwa ta Najeriya (NCC) da hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta ƙasa (NITDA).

MTN da kamfanoni na shirin kara kudin kira

Wannan taro dai na zuwa ne yayin da kamfanonin sadarwa irinsu MTN da Airtel suka buƙaci gwamnatin Najeriya ta amince su kara kuɗin kira, data da tes.

Sun nemi karin kuɗin amfani da layukansu a faɗin Najeriya ne saboda abin da suka kira gaskiyar halin da ake ciki bayan zare tallafin man fetur da faɗuwar ƙimar Naira.

Kara karanta wannan

'Karya ta ƙare': Wasu ƴan Najeriya 2 za su shafe shekaru 40 a gidan yarin Amurka

To sai dai har yanzu gwamnatin tarayya ta hannun hukumar kula da harkokin sadarwa ta ƙasa watau NCC na ganin ƙarin kudin kira ba shi ne mafita ba.

Gwamnati ta ƙi yarda da bukatar kamfannin

NCC ta dage cewa kamfanonin na da wani zaɓin na daban da za su bunƙasa harkokinsu maimakon taba tsarin kudin sadarrwa na 2013 wanda ke aiki har yau

Yanzu haka, ana ci gaba da ganawar tsakanin wakilan gwamnati da kamfanonin sadarwa, inda ake fatan cimma matsaya mai dorewa wadda za ta amfani dukkan ɓangarorin da abin ya shafa.

Wannan al'amari ya kasance abin kallo ga al’umma, ganin yadda sadarwa ke da muhimmanci wajen haɗa kai da ci gaban tattalin arziki a Najeriya.

Kamfanonin sadarwa sun mika koke ga NCC

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kamfanin MTN, Karl Toriola ya tabbatar da cewa kamfanoni sun miƙa bukatar ƙara kudin sadarwa saboda tsadar kaya da faɗuwar Naira.

Kara karanta wannan

Gwamna ya canza sunan jami'a, ya raɗa mata 'Jami'ar Kashim Ibrahim'

A cewar shugaban MTN, haihawar farashin kayayyaki ya shafi kamfanonin sadarwa don haka suke son kara kudin kira da data da kaso 100 a ƙasar nan.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262