Limaman Masallatan Juma'a Za Su Warwasa, Ciyaman Ya Yi Masu Ƙarin Alawus duk Wata

Limaman Masallatan Juma'a Za Su Warwasa, Ciyaman Ya Yi Masu Ƙarin Alawus duk Wata

  • Shugaban ƙaramar hukumar Soba a Kaduna ya karawa limaman masallatan Juma'a alawus din da ake biyansu a wata
  • Hon. Muhammad Ƙawal Shehu ya ce limaman suna ba da gudummuwa wajen isar da manufofin gwamnati ga jama'a da samar da zaman lafiya
  • Limaman Juma'a sun yabawa shugaban ƙaramar hukumar bisa yadda ya ɗauke su da muhimmanci, inda suka ce za su ci gaba da yin bakin ƙoƙarinsu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Kaduna - Shugaban ƙaramar hukumar Soba a jihar Kaduna, Hon. Muhammad Lawal Shehu ya ba da umarnin ƙarawa limaman Juma'a alawus na wata.

Muhammad Lawal ya ce ya tarar da an dakatar da biyan alawus din da ake biyan limaman masallatan Juma'a duk wata a lokacin da ya karɓi mulki.

Taswirar Kaduna.
Shugaban karamar hukumar Soba ya karawa malamai alawus duk wata Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Ciyaman na Soba ya bayyana hakan ne da yake jawabi ga taron limaman Juma'a a sakatariyar Ɗahiru Maigana, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Kara karanta wannan

Shugaban NYSC ya fadi lokacin fara biyan masu yi wa kasa hidima N77,000

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Limanan Juma'a sun samu ƙarin alawus

Hon. Lawal ya bayyana cewa da hawansa mulki, ya gano cewa malaman sun shafe watanni ba tare da biyansu alawus din wata-wata ba, wanda ya ce ba zai yuwu ba.

Ya ce wannan ya sa ya ba da umarnin a duba kuɗin da ake biyan malaman tare da yi masu ƙari saboda halin matsin rayuwa da ake ciki.

A cewarsa, limamai na taka muhimmiyar rawar wajen isar da manufofin gwamnati ga al'umma don haka akwai bukatar ƙara masu ƙwarin guiwa.

Ciyaman na Soba ya jawo Limamai a jiki

"Lokacin da na karɓi ragamar mulki, na ga abin da ake biyan limamai duk wata bai taka kara ya karya ba kuma an ɗauki tsawon watanni ba a biyasu alawus din ba.
"Da na fahimci haka na ce ba zai yiwu ba, yanzu haka mun dawo da biyansu alawus watanni biyu da suka wuce.

Kara karanta wannan

Abuja: Bincike ya yi nisa, an gano wanda ya tashi bom a makarantar Islamiyya

"Sannan na lura cewa abin da ake biyansu bai yi daidai da halin matsin tattalin arzikin da muke ciki ba, kuma na ba da umarnin a masu kari daga wata mai zuwa.," in ji shi.

Hon. Lawal ya yabawa Limamai bisa rawar da suke takawa wajen tabbatar da zaman lafiya a karamar hukumar Soba.

Ya bukace su da su yi amfani da wa’azinsu wajen nasiha ga matasa su guji shaye-shayen miyagun kwayoyi, daba, da sauran ɗabi'u mara kyau domin ci gaban Soba.

Limaman Juma'a sun godewa ciyaman

Da yake jawabi a madadin limaman, babban limamin masallacin Juma’a na Sakaru, Malam Ibrahim Aliyu Bagaldi, ya yabawa ciyaman bisa koƙarin da yake yi na jawo malamai a jiki.

Ya bayyana cewa malaman addinin musulunci a Soba za su yi amfani da matsayinsu wajen yin wa’azin zaman lafiya da addu'ar samun ci gaban karamar hukumar.

Sheikh Ahmad Gumi ya yabi gwamnati

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen malamin addinin Musulunci, Dr. Ahmad Gumi ya ce kafa ma'aikatar dabbobi za ta taimaka wajen magance matsalar tsaro.

Kara karanta wannan

'Na san za a zage ni': Tinubu ya fadi shirin da yake yi wa Najeriya

Sheikh Ahmad Gumi ya kuma yabawa Gwamna Uba Sani na Kaduna bisa matakin da ya ɗauka na tattaunawar sulhu da ƴan bindiga.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262