Mele Kyari: Yadda Almajiri Ya Taso Ya Zama Shugaban NNPCL a Najeriya
- Malam Mele Kyari ya bayyana yadda ya taso daga makarantar almajirai har ya zama shugaban kamfanin makamashi lamba ɗaya a Afirka
- Shugaban kamfanin NNPCL ya ce ya sha ƙalubale a rayuwarsa kafin ya taka matsayin da Allah Madaukakin Sarki ya ba shi a yanzu
- Mele Kyari ya faɗi haka ne yayin da yake murnar cika shekara 60 da haihuwa, wanda ya ce ya tuni ya kai shekarun a kalandar Musulunci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Shugaban kamfanin mai na ƙasa (NNPCL), Malam Mele Kyari ya ba da labarin yadda ya taso daga almajiranci zuwa matakin da yake a yanzu.
Mele Kyari ya bayyana cewa ya tashi daga makarantar Almajirai wacce aka fi sani da Tsangaya har ya zama shugaban kamfanin mai na kasa watau NNPCL
Shugaban NNPCL ya faɗi haka ne a wani saƙo da ya wallafa a shafin X da yake cika shekara 60 da haihuwa a duniya ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban kamfanin NNPCL ya yi almajiranci
Ya bayyana matukar godiya ga Najeriya bisa damar da ya samu tun daga farko har zuwa matsayin da ya taka a yanzu tun da ya gamu da jarabawa kala daban-daban.
Ya godewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da kuma shugaban kasa mai ci Bola Ahmed Tinubu bisa damar da suka ba shi na zama shugaban NNPC.
Yayin da yake tunanin rayuwarsa, Kyari ya ce ya fuskanci lokuta masu kyau da marasa kyau, wahalhalu da nasarori, radadi da farin ciki, gazawa da nasara da sauran ƙalubalen rayuwa.
Ya ce Allah Madaukacin Sarki ne kaɗai ya san irin wahalhalu da jabawar rayuwar da ya tsinci kansa kafin ya taka matsayin da yake a yanzu.
Yadda almajiri ya zama shugaban NNPCL
"Allah SWT cikin falalarsa ya ba ni damar rayuwa har zuwa wannan rana ta musamman, wanda nake cika shekara 60 da haihuwa, na jima da kai wa shekara 60 a kalandar Musulunci.
"Na gode wa ƙasata sosai da ta ba ni damar tashi daga ɗalibin makarantar Almajirai (Tsangaya) zuwa shugaban kamfanin makamashi mafi girma a Afirka.
"Ina matuƙar godiya ga Muhammadu Buhari da Bola Ahmed Tinubu bisa damar da suka ba ni na zama GMD na ƙarshe a NNPC da kuma Shugaba na farko na kamfanin NNPCL."
- Malam Mele Kyari.
"Na fuskanci ƙalubale" - Mele Kyari
Shugaban NNPCL ya ƙara tabbatar da cewa ba a cimma nasara cikin sauki yayin da ya ce ya fuskanci kalubale masu tarin yawa a rayuwarsa.
"Ba zan iya tuna dukkan abubuwan da suka faru da ni a rayuwata zuwa yau ba, na fuskanci lokutan farin ciki da baƙin ciki, wahaloli da nasarori, raɗaɗi da jin daɗi, gazawa da nasarori da kuma sauran abubuwa da yawa da Allah kaɗai ya sani.
"A wannan lokaci, ina jin ya zama wajibi na yi wa al'umma hidima da ƙwarin gwiwa mai ƙarfi fiye da da, tare da fatan samun lada a wurin Allah," in ji shi.
Daga ƙarshe, Malam Kyari ya roki afuwa daga dukkan wanda ya cutar da shi da ba da gangan ba a rayuwarsa.
NNPCL ya fara gyaran matatar Kaduna
A wani labarin, kun ji cewa kamfanin NNPCL ya bayyana cewa an fara gyaran matatar man Kaduna bayan matatun Warri da Fatakwal sun dawo aiki.
Kamfanin mai na ƙasa ya ƙashe maƙudan kudi da suka kai Dala biliyan biyu kafin matatun biyu da ke kudancin Najeriya su farfaɗo su cigaba da aiki.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng