Gwamnan Jihar Bauchi Ya ba Kwamishinonin da Ya Kora Sababbin Mukamai
- Wasu daga cikin tsofaffin kwamishinonin da aka kora sun samu sababbin muƙamai a gwamnatin jihar Bauchi da ke Arewa maso Gabas
- Gwamna Bala Abdulkadir Mohammed ya naɗa uku daga cikin tsofaffin kwamishinonin a matsayin masu ba da shawara na musamman
- Naɗin na su na zuwa ne ƴan awanni kaɗan bayan gwamnan ya yi wa gwamnatinsa garambawul, ya sallami kwamishinoni guda biyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Bauchi - Awanni kaɗan bayan sallamar wasu kwamishinoni, gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed, ya ba wasu daga cikinsu sababbin muƙamai.
Gwamna Bala Mohammed ya amince da naɗin uku daga cikin tsofaffin kwamishinonin a matsayin mashawarta na musamman.
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai ba da shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da hulɗa da jama'a ga gwamnan Bauchi, Mukhtar Gidado, ya fitar, cewar rahoton jaridar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Bala ya yi sababbin naɗe-naɗe
An dawo da tsofaffin kwamishinonin da aka naɗa yanzu a matsayin mashawarta na musamman don su ci gaba da gudanar da aikinsu a cikin gwamnatin.
Tsofaffin kwamishinonin da Gwamna Bala Mohammed ya naɗa a matsayin masu ba da shawara na musamman su ne:
- Abubakar Abdulhameed Bununu - Mai ba da shawara na musamman kan samar da haɗin kan yankuna.
- Kwamared Usman Danturaki - Mai ba da shawara na musamman kan lamuran ma’aikata da tsarin fansho.
- Farfesa Simon Madugu Yalams - Mai ba da shawara na musamman kan ilmin fasaha da sana'o'i
Yaushe naɗinsu zai fara aiki?
A cewar Kwamared Mukhtar Gidado, sababbin naɗe-naɗen za su fara aiki ne nan take, rahoton jaridar The Guardian ya tabbatar.
"Waɗannan naɗe-naɗen, waɗanda za su fara aiki nan take, suna daga cikin ƙoƙarin Gwamna Bala Mohammed na tabbatar da shugabanci mai inganci, haɗin kai, da cimma manufofin ci gaba na gwamnatinsa."
"Gwamna Bala Mohammed ya yi kira ga waɗanda aka nada su yi amfani da iliminsu, jajircewarsu da ƙwarewarsu a fannoni daban-daban domin bayar da gagarumar gudunmawa wajen cimma burinsa na ci gaban jihar Bauchi."
"Gwamnan ya kuma bukace su da su gudanar da aikinsu da ƙwarewa, gaskiya, da kuma himma wajen inganta rayuwar al’ummar jihar Bauchi."
"Haka kuma, Gwamnan ya sake jaddada ƙudirin gwamnatinsa na tabbatar da ingantaccen shugabanci, gaskiya, da ci gaba mai ɗorewa ga ɗaukacin al’ummar jihar Bauchi."
- Kwamared Mukhtar Gidado
Gwamna Bala ya naɗa sabon sakataren gwamnati
A wani labarin da Legit Hausa ta kawo, kun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Mohammed, ya naɗa sabon sakataren gwamnatin jihar (SSG).
Gwamna Bala Mohammeɗ ya amince da naɗin Aminu Hammayo a matsayin sabon sakataren gwamnatin jihar bayan murabus ɗin Barista Kashim Ibrahim.
Hakazalika Gwamna Bala ya maye gurbin babban sakatare ga gwamna, Sama'ila Burga, da Hashimu Kumbala bayan ya yi murabus domin zama shugaban PDP na jihar Bauchi.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng