Gwamnan APC Ya Yi Fallasa, Ya Zargi Ciyamomi da Turawa Shugabannin PDP N12bn

Gwamnan APC Ya Yi Fallasa, Ya Zargi Ciyamomi da Turawa Shugabannin PDP N12bn

  • Gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo, ya yi ƙarin haske kan dalilin dakatar da shugabannin ƙananan hukumomin jihar
  • Sanata Okpebholo ya yi zargin cewa dakatattun shugabannin ƙananan hukumomin sun riƙa tura N12bn ga jagororin PDP a jihar
  • Ya yi zargin cewa an tura kuɗaɗen ta hanyar fakewa da wani aiki, sannan da ka buƙaci su yi bayani sai suka gaza yin hakan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Edo - Gwamnan Jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo, ya zargi dakatattun shugabannin ƙananan hukumomi 18 da karkatar da kuɗaɗe.

Gwamna Monday Okpebholo ya yi zargin cewa a cikin shekara ɗaya da watanni uku, sun ba shugabannin PDP a jihar kuɗaɗen da suka kai sama da N12bn.

Gwamnan Edo ya zargi dakatattun ciyamomi
Gwamna Okpebholo ya zargi dakatattun ciyami da turawa shugabannin PDP N12bn Hoto: @MondayOkpebholo
Asali: Twitter

Gwamnan Edo ya fallasa ciyamomi

Gwamna Okpebholo ya yi wannan zargin ne yayin da ya karɓi baƙuncin shugabannin riƙo na ƙananan hukumomi 18 da kansiloli waɗanda suka kai masa ziyara a gidan gwamnati, cewar rahoton jaridar Tribune.

Kara karanta wannan

Rikici da gwamna ya jawo an tsige shugabannin kananan hukumomi daga muƙamansu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yabawa shugabannin riƙon da kansilolin bisa jarumtarsu wajen kare dimokuradiyya da tabbatar da gaskiya a matakin ƙananan hukumomi, rahoton Vanguard ya tabbatar.

Gwamnan Okpebholo ya jaddada cewa kuɗaɗen ƙananan hukumomi ba wanda ya isa ya yi kaka-gida a kansu, duk kuwa matsayin da yake da shi.

"Lokacin da na shiga ofis, na yi taro da Akanta Janar, kuma ya nuna mani wasu takardu.Wasu daga cikin kuɗaɗen da aka kashe ba su da cikakken bayani."
"Hankali na ya karkata kan wasu kuɗaɗe da aka kashe, da aka ce kuɗaɗen tsaron muhalli ne."
“Ban taɓa jin wannan ba a baya, kuma adadin kuɗin yana da yawa, N800m a duk wata. Waɗannan shugabannin ƙananan hukumomi suna tara waɗannan kuɗaɗen suna ba wa shugabannin wata jam’iyya."

- Gwamna Monday Okpebholo

Wane mataki Gwamna Okpebholo ya ɗauka?

Gwamnan ya ce gano hakan ya sanya ya yi taro da tsofaffin shugabannin ƙananan hukumomi inda aka buƙaci su yi bayanin kudaden da aka ware don "Tsaron Muhalli", amma suka gaza yin hakan.

Kara karanta wannan

Ana batun tsadar mai, gwamnatin Sokoto ta samar da shirin saukaka zirga zirga

“Na gayyaci shugabannin ƙananan hukumomin, amma ba mu yi taro da su ba, sai mataimaki na ya yi taro da su. Ya buƙaci su yi bayani, amma babu wanda ya iya ba da bayani."
"Ya buƙace su kawo takardunsu, sun amince inda suka ce za su kawo cikin awanni 24, amma mataimaki na ya ce an ba su awanni 48."
"Amma waɗannan shugabannin ba su bi wannan umarnin ba har tsawon makonni biyu, kuma babu wanda ya kawo lissafin kudinsa."
"Sakamakon haka, na aikawa hukumar yaƙi da masu yi wa tattalin arziƙin ƙasa ta'annati (EFCC) wasiƙa don su duba yadda suka kashe kuɗaɗen."
“Kasancewa ta tsohon ɗan majalisa, na san akwai hukuma mai ikon kula da su, don haka na aikawa majalisar dokokin jihar Edo (EDHA) wasiƙa, suka gayyace su, amma sai suka ƙi zuwa, daga nan aka dakatar da su na tsawon watanni biyu."

- Gwamna Monday Okpebholo

An tsige ciyamomi a jihar Edo

Kara karanta wannan

Wasu dattawa sun bukaci yi wa sanatan PDP kiranye, sun fadi dalilansu

A wani labarin kuma, kun ji cewa takun saƙar da ake yi tsakanin gwamnan jihar Edo, Monday Okpebholo da shugabannin ƙananan hukumomi ya ƙara tsananta.

Tsanantar rikicin ta jawo an tsige shugabannin ƙananan hukumomin Esan ta Arewa maso Gabas da Akoko-Ado daga kan muƙamansu.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng