Shugaban NYSC Ya Fadi Lokacin Fara Biyan Masu Yi Wa Kasa Hidima N77,000

Shugaban NYSC Ya Fadi Lokacin Fara Biyan Masu Yi Wa Kasa Hidima N77,000

  • Shugaban hukumar NYSC ya kwantar da hankalin matasa masu yi wa ƙasa hidima da ke jiran a fara biyansu alawus na N77,000 duk wata
  • Birgediya Yusha'u Ahmed ya ba da tabbacin cewa nan ba da jimawa ba matasan da ke hidimtawa za su fara karɓar sabon alawus ɗin daga gwamnatin tarayya
  • Shugaban na NYSC ya bayyana zai ba da fifiko wajen kare rayuka da jin daɗin matasan ta hanyar tabbatar da sun samu haƙƙokinsu

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaban hukumar masu yi wa ƙasa (NYSC), Birgediya Janar Yushau Ahmed, ya yi magana kan lokaci fara biyan sabon alawus ga ƴan bautar ƙasa.

Shugaban na NYSC ya tabbatarwa matasa masu yi wa ƙasa hidima cewa za su fara karɓar mafi ƙarancin albashi na N77,000

Za a biya masu NYSC N77,000
Yusha'u Ahmed ya ce an kusa fara biyan masu NYSC N77,000 Hoto: @officialnyscng
Asali: Twitter

Yaushe za a fara biyan masu NYSC N77,000

Kara karanta wannan

Kaduna: Sanatan PDP ya yi martani kan shirin yi masa kiranye daga majalisa

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa shugaban na NYSC ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a Abuja wajen ƙaddamar da motar ma'aikata da kamfanin inshorar Capital Express ya ba hukumar kyauta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Birgediya Janar Yusha'u Ahmed ya bayyana cewa an kammala shirye-shiryen biyan ƙarin alawus ɗin matasan da ke yi wa ƙasa hidima.

Ya tabbatarwa matasan masu NYSC cewa fifikonsa shi ne tsaronsu da jin daɗinsu, don haka a shekarar 2025 za su samu dukkan abubuwan da suka dace da su.

Birgediya Janar Yusha'u Ahmed ya bayyana cewa an ba da motar ne ga hukumar don ma’aikata, sannan an yi hakan ne don rage matsalolin sufuri da suke fuskanta.

Ya ce ma’aikatan hukumar da kuma 'yan NYSC suna yawan ƙorafin cewa suna fuskantar matsaloli wajen jigilar kansu zuwa da dawowa daga ofis.

Meyasa aka ba NYSC kyautar mota

A nasa ɓangaren, shugaban kamfanin Inshorar Capital Express, Mista Matthew Ogwezhi, ya ce NYSC da kamfaninsa sun jima suna yin haɗin gwiwa.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya fadi abin da sukar gwamnatin Tinubu ya janyo masa

Ya ce gudunmawar motar tana daga cikin hadin gwiwar da suke yi don tallafawa ayyukan hukumar NYSC.

Mista Mathew Ogwezhi ya ce kamfanin ya ba da wannan gudunmawar ne don tallafawa jigilar ma’aikata zuwa wurin aiki da kuma dawowa, duba da tsadar man fetur da sufuri a birnin Abuja.

Ya ce kowace ƙungiya tana barin wani tarihi mai kyau ne ta hanyar tasirin da take yi a cikin al’umma, don haka ya zama wajibi a riƙa ba wa al’umma gudunmawa.

Masu NYSC sun roƙi gwamnati

A wani labarin kuma, kun ji cewa matasa masu yi wa ƙasa hidima (NYSC) sun miƙa ƙoƙon bararsu ga gwamnatin tarayya kan fara biyansu alawus na N77,000.

Matasan sun buƙaci gwamnatin tarayya da ta fara biyansu N77,000 domin N33,000 da ake biyansu ta yi musu kaɗan domin ba ta isarsu.

Sun bayyana cewa duk da gwamnatin tarayya ta amince da sabon mafi ƙarancin albashi, har yanzu ba a fara biyansu N77,000 duk wata ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng