Najeriya Ta Kara Yin Babban Rashi, Allah Ya Yi Wa Tsohon Kwamishina Rasuwa

Najeriya Ta Kara Yin Babban Rashi, Allah Ya Yi Wa Tsohon Kwamishina Rasuwa

  • Tsohon kwamishinan ayyuka da sufuri na jihar Benuwai, Farfesa Joseph Orkar ya mutu a ƙarshen makon da ya gabata
  • Gwamna Hyacinth Alia ya yi alhinin wannan rashe, ya roki Allah ya bai wa iyalansa da al'ummar jihar Benuwai baki ɗaya haƙuri
  • Ya ce marigayin jagoran al'umma ne wanda ya yi amfani da ƙwarewarsa da hikimarsa wajen gina rayuwar mutane da yawa a zamanin rayuwarsa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Benue - Wani tsohon kwamishinan jihar Benuwai da ke Arewa ta Tsakiya a Najeriya, Farfesa Joseph Orkar ya riga mu gidan gaskiya.

Farfesa Orkar, babban yayan Gideon Orkar, jagoran juyin mulkin 1990, ya mutu ne ranar Lahadi, 5 ga Janairu, 2025.

Gwamna Alia na jihar Benuwai.
Tsohon kwamishina a jihar Benuwai ya rasu, gwamna ya yi ta'aziyya Hoto: Hyacinth Lormem Alia
Asali: Facebook

Gwamna Alia ya yi alhinin rasuwar Orkar

Gwamnan jihar Benuwai, Hyacinth Alia ya yi alhini wannan rashi tare da miƙa sakon ta'aziyya ga iyalan marigayin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Gwamna Radda ya yi garambawul a gwamnatinsa, ya shawarci sabon kwamishina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Benuwai, Tersoo Kula ya fitar yau Talata,

Gwamna Hyacinth Alia, ya bayyana marigayin a matsayin shugaba kuma jagoran al’umma, uba kuma wanda ya gina rayuwar mutane da yawa.

Tsohon kwamishinan ya taimaki mutane

Ya kara da cewa tasirin marigayin a matsayinsa na dan siyasa kuma ma'aikacin gwamnati, ya wuce iyakar danginsa da makusanta, ya shafi al'umma gaba ɗaya.

Hyacinth Alia ya ce:

"A matsayinsa na tsohon kansilan gundumar Ugondo/Mbasambo da ke ƙaramar hukumar Gwer, ɗan majalisar dokokin jihar Benuwai mai wakiltar Makurdi a 1979.
"Sannan kuma kwamishinan ayyuka a sufuri a gwamnatin Aper Aku, Farfesa Orkor ya nuna gogewa, ilimi, hikima da jagoranci na gari wajen amfanar da al'umma."
"Kasancewar Farfesa na farko a ƙabilar Tiv’, za a rika tunawa da Orkar saboda wasu kyawawan wallafe-wallafen da ya yi a Tiv, ya rubuta littattafai da yawa da aka wallafa a cikin harshen Tiv.

Kara karanta wannan

Rikici ya ɓarke tsakanin gwamna a Arewa da mai martaba Sarki? Bayanai sun fito

Gwamna ya miƙa sakon ta'aziyya da addu'a

Gwamna Alia ya yi addu'ar Allah ya bai wa iyalansa, ƴan uwa da abokan arziki da baki ɗaya al'ummar Makurɗi hakuri da juriyar rashin uba kuma jagora.

Kakakin gwamnan ya ƙara da cewa:

"Mai girma gwamna ya kuma yi addu’ar Allah ya ba iyalansa, al’ummar karamar hukumar Makurdi da jihar Binuwai baki daya haƙurin wannan rashi, ya kuma bai wa Farfesa Orkar hutu na har abada.”

A hirarsa ta karshe da jaridar Punch kimanin shekaru hudu da suka gabata, Farfesa Orkar ya bayyana yadda Janar Ibrahim Babangida (mai ritaya) ya tsare shi.

Ya ce tsohon shugaban ƙasa na mulkin sojan ya tsare shi a kurkuku ne bayan juyin mulkin 1990 wanda kaninsa, Manjo Gideon Orkar ya jagoranta.

Sakataren gwamnatin Ondo ya cika a asibiti

Kun ji cewa hatsarin mota ya yi sanadiyyar rasuwar sakataren gwamnatin jihar Ondo da ke Kudu maso Yamma, Temitayo Oluwatuyi Oluseye.

Kara karanta wannan

Kwana ya kare: Tsohon sakataren gwamnatin jiha a Najeriya ya rasu

Marigayin ya gamu da hatsari ne a ranar 15 ga watan Disamba, 2024 yayin da rai ya yi halinsa a asibiti ranar Asabar da ta shuɗe.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262