'Yan Bindiga Sun Dauko Salon Fadada Ta'addanci zuwa Kudancin Najeriya

'Yan Bindiga Sun Dauko Salon Fadada Ta'addanci zuwa Kudancin Najeriya

  • Gwamna Seyi Makinde ya ce ‘yan bindiga daga yankin Arewa maso Yamma suna neman mafaka a jihar Oyo sakamakon matsin lamba daga sojoji
  • Seyi Makinde ya tabbatar wa da al’ummar jihar cewa gwamnati za ta yi duk mai yiwuwa domin hana ‘yan bindigar samun mafaka a jihar Oyo
  • Gwamnan ya yi alkawarin ganin cewa wadanda suka haddasa hatsarin turmutsitsi a makarantar Musulunci ta Bashorun za su fuskanci hukunci

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Oyo - Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana damuwa kan fitar wasu ‘yan bindiga daga yankin Arewa Maso Yamma zuwa jihar Oyo sakamakon hare-haren sojoji a sansaninsu.

Seyi Makinde ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta dauki tsauraran matakai domin ganin an kakkabe ‘yan ta’addan daga jihar.

Kara karanta wannan

Miyagun ƴan bindiga sun kafa sansani a kusa da inda gwamna ya shirya biki

Makinde
'Yan bindiga sun fara kaura jihar Oyo. Hoto: Seyi Makinde
Asali: Twitter

Jaridar Punch ta wallafa cewa gwamna Seyi Makinde ya yi bayanin ne yayin wani taron addu'o'i da aka shirya a jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan bindiga sun fara hijira zuwa Oyo

A yayin taron addu’o’i da aka gudanar a Sakatariyar Jihar Oyo a Agodi, Ibadan, Seyi Makinde ya bayyana cewa an samu rahotanni kan yadda wasu ‘yan bindiga ke komawa jihar.

“Mun samu labari daga wani taron tsaro cewa wasu miyagun mutane daga Arewa maso Yamma suna shigowa jihar nan saboda matsin lamba daga sojoji,”

- Seyi Makinde

Daily Post ta wallafa cewa gwamnan ya kara da cewa hare-haren sojoji da suka hada da ruwan bama-bamai sun tilasta wa miyagun neman mafaka a wasu jihohi.

Sai dai gwamnan ya tabbatar wa da al’ummar jihar cewa za su gano 'yan ta'addar, su kuma yi maganinsu.

Karfafa tsaro da gargadi ga al’umma

Seyi Makinde ya bayyana cewa a shekarar 2024, jihar ta fuskanci kalubale iri-iri, ciki har da rikice-rikicen tsaro, amma ya yi alkawarin kara kokari a 2025.

Kara karanta wannan

Gwamna ya fusata da kashe bayin Allah, ya sanya dokar zaman gida a jiharsa

Gwamnan ya ba da misalin yadda a lokacin wani taron da aka yi domin murnar ranar haihuwarsa aka samu sansanin ‘yan bindiga da ke nisan kasa da kilomita biyu daga wurin.

“Ga sarakunan gargajiya da kuma al’ummar jihar, idan kun ga wani abu da ba ku yarda da shi ba, ku sanar da hukumomi nan take. Jihar Oyo ba wurin zama ba ce ga ‘yan bindiga,”

- Seyi Makinde

Magana kan hatsarin makarantar Bashorun

Makinde ya nuna bacin ransa game da hatsarin da ya faru a makarantar Musulunci ta Bashorun, inda yara 35 suka rasa rayukansu a watan Disamba.

“Wani ya ce min irin wannan abu ya faru a Anambra da Abuja amma ba a dauki mataki ba. Na ba shi amsa cewa Jihar Oyo ba Anambra ba ce, kuma ba Abuja ba ne,”

- Seyi Makinde

Gwamnan ya ce ba ya adawa da bayar da beli ga wadanda ake zargi, amma yana bukatar ganin shari’a ta ci gaba ba tare da katsalandan ba.

Kara karanta wannan

Barazanar tashin bam: Gwamnatin Neja ta aika da muhimmin gargadi ga manoma

Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana kan tsaro

A wani rahoton, kun ji cewa, Sheikh Ahmad Gumi ya ba gwamnatin tarayya shawara kan yadda za a magance matsalar tsaro a kasar nan.

Malamin ya ya bayyana cewa samar wa matasa abin yi hanya ce da za ta taimaka matuka wajen rage yaduwar ta'addanci a fadin Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng