JAMB Ta Tatso Naira Biliyan 22, Ta Tura Naira Biliyan 6 a Asusun Gwamnati a 2024
- Hukumar JAMB ta sanar da tura N6,034,605,510.69 ga baitulmalin kasa daga rarar kuɗaɗen da ta samu a shekarar 2024
- Rahoton da aka fitar na mako-mako ya ce rage N1,500 kan fom din UTME ga dalibai ya sa gudunmawar JAMB ta kai N9,013,068,510.69
- Karkashin jagorancin Farfesa Is-haq Oloyede, JAMB ta ce ta bayar da gudunmawar fiye da N50bn tun daga shekarar 2016
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT, Abuja - Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i da Manyan Makarantu (JAMB) ta sanar da biyan fiye da Naira biliyan 6 ga asusun gwamnatin tarayya a shekarar 2024.
Wannan na kunshe a cikin rahoton mako-mako na hukumar ta fitar ranar Litinin ta hannun mai ba da shawara kan harkokin yada labarai, Dakta Fabian Benjamin.
Daily Trust ta wallafa cewa Dakta Benjamin ya ce hukumar JAMB ta samar da jimillar kudaden shiga na N22,996,653,265.25 a 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya kara da cewa daga cikin wannan kudade, an aika akalla N6,034,605,510.69 ga asusun gwamnatin tarayya a shekarar da ta gabata.
Yadda hukumar JAMB ta samu kudi
Jaridar The Sun ta wallafa cewa hukumar JAMB ta bayyana yadda ta yi nasarar samun biliyoyin Naira daga daliban Najeriya a shekarar 2024.
Ta kara da cewa rage kudin fom na UTME da N1,500 ga kowane ɗalibi, wanda aka ninka da adadin waɗanda suka sayi fom din ya habaka kudin da suka samu a bara.
Mai ba da shawara kan harkokin yada labaran hukumar, Dakta Fabian Benjamin ya ce kudin a wannan tsari ya karu zuwa N9,013,068,510.69.
JAMB ta mika kudi ga gwamnati
Hukumar JAMB ta ce adadin kudin da ta mika ga gwamnati ya fito daga rarar kuɗin da tattaro bayan gudanar da Jarabawar Shiga Manyan Makarantu ta 2024 cikin nasara.
JAMB ta kara da cewa ta bayar da gudunmawar fiye da Naira biliyan 50 ga baitulmalin ƙasa a cikin shekaru bakwai da suka gabata ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Farfesa Is-haq Oloyede.
Hukumar JAMB ta bayyana kudin da ta samu
Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Jami’o’i da Manyan Makarantu (JAMB) ta bayyana cewa akwai bukatar ta bayyana gaskiyar yadda ta ke gudanar da ayyukanta.
Hukumar ta ce;
“Yayin da muke duban shekarar 2024, yana da muhimmanci mu ci gaba da nuna gaskiya ta hanyar bayyana irin yadda muka gudanar da harkokin kuɗaɗenmu a shekara.
“A shekarar 2024, hukumar ta samar da jimillar kudaden shiga na N22,996,653,265.25. A cikin wannan shekarar, hukumar ta tura N6,034,605,510.69 ga gwamnati.
“Idan aka haɗa da rage kudin fom na N1,500 ga ɗalibai wanda aka ninka da yawan waɗanda suka ci gajiyar hakan a 2024, jimillar kudin da JAMB ta tura zai kai N9,013,068,510.69.”
JAMB ta fadi masu sake jarrabawa
A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumar shirya jarabawar shiga jami’o’i da manyan makarantu (JAMB) ta bayyana cewa dalibai 80,166 ne za su sake zana jarabawar UTME
JAMB ta bayyana hakan ne a wata sanarwa da ta fitar, ta tabbatar wa daliban da abin ya shafa cewa an shirya duk abin da ake buƙata don tabbatar da cewa za su yi jarabawar cikin nasara.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng