Buhari Ya Yi Ta'azziya bayan Rasuwar Mahaifiyar Ministan Tinubu, Ya Fadi Alherinta

Buhari Ya Yi Ta'azziya bayan Rasuwar Mahaifiyar Ministan Tinubu, Ya Fadi Alherinta

  • Tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jajanta rasuwar Hajiya Hauwa’u Abubakar, mahaifiyar Ministan Kwadago, Alhaji Maigari Dingyadi
  • A wata tattaunawa ta waya da Ministan tarayyar, Dingyadi, Buhari ya nuna alhininsa, tare da yi wa mamaciyar addu’a na samun rahama da dacewa
  • Buhari ya ce tsawon rayuwar Hajiya Hauwa’u ta nuna jajircewa kan iyali da al’umma, kuma ta bar darussa masu muhimmanci ga al’ummomi na gaba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Daura, Katsina - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nuna alhinin rasuwar mahaifiyar tsohon Ministansa wanda ke riƙe da mukamin a gwamnatin Bola Tinubu.

Buhari ya bayyana rasuwar Hajiya Hauwa’u Abubakar, mahaifiyar Ministan Kwadago, Alhaji Maigari Dingyadi a matsayin babban rashi.

Buhari ya yi ta'azziyar rasuwar mahaifiyar Ministan Tinubu
Muhammadu Buhari ya tura sakon ta'azziya ga Minista Maigari Dingyadi bayan rasuwar mahaifiyarsa. Hoto: Muhammadu Buhari.
Asali: Facebook

Muhammadu Buhari ya kira tsohon Ministansa a waya

A cikin wata sanarwa da hadiminsa, Garba Shehu ya wallafa a shafin X, ya bayyana marigayiyar a matsayin abin koyi.

Kara karanta wannan

Sheikh Ahmad Gumi ya yi magana kan tsaro yayin da sojoji ke kokarin cafke Turji

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Buhari ya bayyana Hajiya Hauwa’u a matsayin wata mace da ta kasance abin koyi ga mutane saboda dabi’unta na kirki da jajircewarta kan iyali da al’umma.

A ranar Lahadi 5 ga watan Janairun 2025, Buhari ya kira Minista Dingyadi ta waya inda ya yi masa ta'azziya.

Buhari ya kadu da rasuwar mahaifiyar Minista Dingyadi

Tsohon shugaban kasar ya nuna damuwarsa kan wannan babban rashi da aka yi ga iyali da kuma al’ummar kasa.

Ya kuma ce irin rayuwar da Hajiya Hauwa’u ta yi tana cike da darussa masu muhimmanci da za su kasance jagora ga mutane masu tasowa.

Buhari ya bayyana cewa tsawon rayuwar mamaciyar alama ce ta nuna muhimmancin ciyar da iyali gaba da kyautata al’amuran zamantakewa.

Ya ce irin wadannan dabi’u suna taimakawa wajen gina al’umma mai kyau kuma za su ci gaba da kasancewa abin koyi ga matasa.

Tsohon shugaban kasa ya yi addu'a ga marigayitar

Kara karanta wannan

Ganduje ya yi wa Kwankwaso shagube, ya yi barazanar kwace Kano a zaben 2027

A sakonsa, tsohon shugaban kasar ya kuma yi addu’ar neman rahamar Allah ga mamaciyar tare da fatan Allah ya ba ta aljanna Firdausi.

Buhari ya kuma yi wa Minista Dingyadi ta’aziyya da kuma fatan Allah ya ba shi da iyalinsa hakuri da juriyar wannan babban rashi.

Wannan rasuwa, a cewarsa, babbar asara ce ba kawai ga iyalin Dingyadi ba, har ma ga daukacin al’umma baki daya.

Ya kuma tunatar da al’umma cewa rayuwa mai kyau irin ta Hajiya Hauwa’u na da darasi ga kowa, musamman wajen ciyar da al’umma gaba.

Buhari ya jajantawa Gwamna Namadi na Jigawa

A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi ta'azziyar rasuwar mahaifiyar Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa da dansa.

Buhari ya ce mutuwar dattijuwar da dansa al’amari ne da Allah ya kaddara wanda babu yadda aka iya, dole a rungumi kaddara.

Kara karanta wannan

Peter Obi ya ziyarci IBB, ya bayyana abubuwan da suka tattauna a kan Najeriya

Tsohon shugaban kasar ya ce mutuwar mahaifiya da ɗa a rana guda abu ne mai ciwo, ya shawarci gwamnan da dauki hakan a matsayin jarabawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.