Peter Obi Ya Fadi Abin da Sukar Gwamnatin Tinubu Ya Janyo Masa
- Jigo a jam'iyyar adawa ta LP, Peter Obi ya faɗi halin da ya tsinci kansa a ciki saboda sukar gwamnatin Bola Tinubu
- Ɗan takarar shugaban ƙasan na zaɓen 2023 ya bayyana cewa ana yi wa rayuwarsa barazana saboda fitowa ya faɗi gaskiya
- Sai dai, ya bayyana cewa ba zai tsorata ba wajen faɗin gaskiya duba da halin da ƙasar nan ta tsinci kanta a ciki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi magana kan barazanar da ake yi wa rayuwarsa.
Peter Obi ya bayyana cewa saƙon da ya fitar na sabuwar shekara, kan halin da ƙasar nan take ciki a ƙarƙashin Bola Tinubu, ya janyo masa barazana ga rayuwarsa da ta iyalansa.
An yi wa Peter Obi barazana
Peter Obi ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a wani rubutu da ya yi a shafinsa na X.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya ce ya samu nau’o’in saƙonni iri-iri, har da na barazana ga rayuwarsa da ta waɗanda ke kusa da shi.
Peter Obi ya caccaki gwamnatin Tinubu
A saƙonsa na sabuwar shekara, Peter Obi ya dage cewa halin matsin tattalin arziƙi a Najeriya ya ƙara taɓarɓarewa duk da iƙirarin da gwamnatin tarayya ke yi na cewa manufofinta suna yin aiki.
Ya kuma ce ƙasar nan na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan ƙasashe masu talauci a duniya.
Peter Obi ya yi suka kan Shugaba Bola Tinubu, inda ya buƙace shi da ya daina tafiye-tafiye zuwa ƙasashen waje sannan ya riƙa tsayawa ana duba lafiyarsa a Najeriya.
Sai dai, yayin wata hira da aka yi da shi, mai magana da yawun jam'iyyar APC, Felix Morka, ya ce Peter Obi yana ƙetare iyaka da yawan sukar da yake yi wa APC da gwamnatin Tinubu.
Da yake mayar da martani kan kalaman Morka, Peter Obi ya ce ya kamata a bayyana masa ko ya ƙetare iyaka, inda ya sake wallafa saƙonsa na sabuwar shekara kuma ya buƙaci ƴan Najeriya su nuna masa inda ya wuce gona da iri.
Wane hali rayuwar Peter Obi ke ciki?
“Shin na ƙetare iyaka kuwa? Na yi wannan tambayar ne saboda saƙona na sabuwar shekara ya janyo barazana ga rayuwata, iyalina, da waɗanda ke kusa da ni."
“Duk da cewa na samu saƙonni iri-iri, wani mai suna Felix Morka ya yi zargin cewa na ‘ƙetare iyaka’ tare da gargaɗin cewa zan ɗanɗana kuɗata."
“Na ga ya zama dole in sake sanya wannan saƙo tare da kira ga duk wanda bai duba ba ya kalla. Idan na ƙetare iyaka, ina gayyatar kowa ya nuna min inda hakan ya faru, domin a shirye na ke na ci gaba da mutunta doka."
- Peter Obi
Sai dai Obi ya jaddada cewa ba za a iya tsoratar da shi har ya daina bayyana gaskiya ba, musamman yayin da ƙasar ke ci gaba da fuskantar abubuwan da suka saɓa ƙa’idojin dimokuraɗiyya.
Peter Obi ya ziyarci IBB
A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Anambra kuma jigo a jam'iyyar LP, Peter Obi, ya ziyarci tsohon shugaban ƙasa, Ibrahim Badamasi Babangida.
Peter Obi wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a zaɓen shekarar 2023, ya bayyana cewa ya yi ziyarar ne domin tabbatar da jajircewarsa kan gina ƙasa.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng