Abin Fashewa Ya Tarwatse a Jihar Ribas, Ya Rutsa da Mutane 20

Abin Fashewa Ya Tarwatse a Jihar Ribas, Ya Rutsa da Mutane 20

  • kalla mutum 20 ne suka jikkata, ciki har da wata mace mai juna biyu d sakamakon fashewar tukunyar iskar gas a garin Fatakwal
  • Tukunyar gas din da ta fashe a lokacin da ake tsaka da gyaranta ya jawo gagarumar matsala, inda ta rusa wasu shugunan da ke kusa
  • Duk da haka, har yanzu rundunar 'yan sandan Jihar Ribas ba ta fitar da karin bayani game da wannan mummunan lamari ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Rivers - Wani mummunan lamari da ya auku a garin Fatakwal, hedikwatar Ribas, yayin da abin fashewa da aka tabbatar da tukunyar iskar gas ne ya tarwatse.

Mutane akalla 20 su ka jikkata daga fashewar da auku, daga cikinsu har da wata mace mai juna biyu da ’ya’yanta hudu, da kuma wasu ma’aurata.

Kara karanta wannan

Tinubu: Kalaman Peter Obi sun yi wa APC zafi, ta zarge shi da son tunzura jama'a

Rivers
Tukunyar gas ta fashe a Ribas Hoto: Legit.ng
Asali: Original

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a yankin Orazi, inda aka tura wadanda abin ya rutsa da su zuwa Asibitin Koyarwa na Jami’ar Fatakwal.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda tukunyar gas ta fashe a Ribas

An gano cewa tukunyar iskar gas din ta fashe ne a wani shagon sayar da iskar gas a lokacin da wani ma’aikaci ke gyara tukunyar da ta lalace.

Fashewar tukunyar ta yi bindiga sosai, wanda ya janyo tarwatsewar gine-gine da kuma lalacewar kayan more rayuwa a wurin.

Wannan lamarin ya sa jama’a, ciki har da wajen shagon gudun neman tsira yayin da su ka fada a cikin mummunan firgici da dimuwa.

Jama’a sun raunata a jihar Ribas

Fashewar tukunyar iskar gas din ya janyo manyan raunuka ga mutane da dama, inda suka samu raunuka a jikinsu.

Tashin wutar ya haddasa lalacewar ƙonewar wasu kayan abinci da kayan aiki da ke cikin shagon, inda jama’a suka shiga wani hali.

Kara karanta wannan

Daga zuwa sasanta rikicin miji da mata, an kashe wani malamin addini a Najeriya

Mutane sun shiga rudani a Ribas

Mace mai juna biyu da lamarin ya rutsa da ita ya hada har da ’ya’yanta hudu, da kuma wasu ma’aurata, wadanda duk sun samu raunuka a jikin su.

Wani daga cikin dan uwan iyalan wanda abin ya rutsa da su ya bayyana cewa har yanzu sun kashe sama da N500,000 wajen biyan kudin magani a asibiti.

Ya kara da cewa:

"Kira na aka yi cewa dan uwana da matarsa suna cikin wadanda abin ya rutsa da su, yana mai cewa yana cikin matsananciyar damuwa game da yadda lamarin ya shafi danginsa."

Ana jiran martanin 'yan sandan Filato

Rundunar 'yan sandan jihar Filato ba ta yi karin bayani a kan mummunan lamarin da ya afku har ta kai ga jikkatar mutane akalla 20, wanda yanzu ke karbar magani daga jami'an lafiya.

Rahotanni sun ce ana jiran jami'ar hulda da jama'a na rundunar ’yan sandan Jihar Ribas, Grace Iringe-Koko domin samun sahihin bayanin dalilan da ya haddasa mummunan fashewar.

Kara karanta wannan

2025: Farfado da tattalin arziki da batutuwa 9 da Tinubu ya yi a sakon sabuwar shekara

Kotu a Ribas ta kori shugabannin APC

A baya, mun ruwaito cewa Babbar kotun Ribas mai zama a Fatakwal ta soke tarukan da jam’iyyar APC ta gudanar don zaɓen shugabannin jihar, wanda hakan ya rushe nasarar Cif Tony Okocha.

Mai shari'a Godswill Obomanu ya bayyana cewa kotun ta soke tarukan ne saboda raina umarnin da ta bayar a baya, wanda ya hana jam’iyyar gudanar da zaɓen shugabanni a jihar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.