Gwamna Ya Dakatar da Sarki da Majalisarsa bayan Korafin Jama'a

Gwamna Ya Dakatar da Sarki da Majalisarsa bayan Korafin Jama'a

  • Gwamna Bassey Otu na jihar Cross River ya dakatar da Hakimin Esuk Utan, Okon Archibong, tare da majalisarsa bisa zargin yin ba daidai ba a ofis
  • An umurci Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Karamar Hukumar Calabar da ta binciki zargin tare da mika rahoto kan lamarin cikin mako guda
  • An ruwaito cewa kwamitin da za a nada mai mutane biyar zai kula da harkokin kauyen Esuk Utan yayin da ake jiran sakamakon binciken

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Cross Rivers - Gwamnan jihar Cross River, Bassey Otu, ya amince da dakatar da Hakimin Esuk Utan, Cif Okon Archibong, tare da majalisarsa nan take.

Dakatarwar ta biyo bayan zarge-zargen amfani da ofis ba bisa ka’ida ba, wanda ya jawo korafe-korafe da dama daga mazauna yankin.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Kano ya yi murabus bayan dakatar da shi daga NNPP

Gwaman Cross rivers
An dakatar da basarake a Cross Rivers. Hoto: Bassey Otu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa matakin ya fito ne daga wata sanarwa da jami'in yada labaran gwamnan, Mista Nsa Gil, ya fitar ranar Litinin a birnin Calabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilin dakatar da hakimin Esuk Utan

Gwamnatin Cross Rivers ta ce akwai zarge-zarge masu yawa da aka gabatar kan yadda Hakimin Esuk Utan, Cif Okon Archibong, da majalisarsa ke tafiyar da al’amuran yankin.

The Guardian ta wallafa cewa gwamna Otu ya umurci Majalisar Sarakunan Gargajiya ta Karamar Hukumar Calabar da ta gudanar da bincike mai zurfi kan zarge-zargen.

Haka zalika, majalisar za ta mika rahoton bincike tare da shawarwari cikin mako guda ga ofishin mai bai wa gwamna shawara kan harkokin sarauta.

Sanarwar ta ce:

“Kwamitin zai aika rahoton binciken tare da shawarwari zuwa ofishin mai bai wa gwamna shawara kan harkokin sarautu cikin mako guda.”

Kwamitin wucin gadi domin kula da Esuk Utan

Kara karanta wannan

Tinubu na ganin sabuwar matsala daga Arewa, dattawa sun ƙi yarda da gyaran haraji

Domin tabbatar da cigaban gudanar da harkokin yau da kullum na Esuk Utan, gwamnan ya umarci a kafa kwamitin mutane biyar domin kula da harkokin yankin.

Wannan kwamitin zai kasance a matsayin jagoran wucin gadi har sai an kammala binciken da aka fara kan hakimin da majalisarsa.

“Majalisar Kabilar Obutong za ta kafa kwamitin mutane biyar domin kula da harkokin Esuk Utan yayin da ake jiran sakamakon bincike.”

- Gwamna Otu

Kira ga mazauna Esuk Utan

Gwamna Otu ya yi kira ga mazauna yankin Esuk Utan da su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da wata matsala ba.

Haka kuma, ya gargadi al’umma da masu gudanar da kasuwanci a yankin da su daina yin hulɗar sarauta da hakimin da majalisarsa da aka dakatar.

Ya ce:

“Mazauna yankin da ‘yan kasuwa su ci gaba da ayyukansu cikin kwanciyar hankali tare da dakatar da duk wata hulda da hakimin da majalisarsa da aka dakatar.”

Kara karanta wannan

An ware biliyoyi domin yin hidima ga Akpabio, Barau da sauran shugaban majalisa

An yi duka ga basarake a jihar Osun

A wani rahoton, kun ji cewa wani basarake a jihar Osun ya bayyana yadda wasu yan daba suka masa dukan kawo wuka a fadarsa.

Oba Jelili Olaiya ya ce yan daba sun kai masa hari tare da yin dukan tsiya ga matarsa a gaban jami'an tsaro 18 ba tare da an dauki mataki ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng