Kotu Ta Ci Taran Mutanen Wike da Suka so Jefa Fubara a Matsala kan Kasafin Kudi

Kotu Ta Ci Taran Mutanen Wike da Suka so Jefa Fubara a Matsala kan Kasafin Kudi

  • Kotun jihar Rivers ta yanke hukunci cewa Gwamna Siminalayi Fubara yana da ikon gudanar da mu'amala da 'yan majalisa marasa rinjaye
  • Mai shari’a Sika Aprioku ta bayyana cewa kafin kotun koli ta yanke hukunci, gwamna zai iya aiki da majalisa mai 'yan majalisi uku
  • Kotun ta yi watsi da karar da ke neman a tilasta wa gwamnan sake gabatar da kasafin kudin 2024 ga majalisar da ke biyayya ga Nyesom Wike

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Rivers - Kotun jihar Rivers ta yi hukuncin cewa gwamna Siminalayi Fubara yana da ikon gudanar da harkokin gwamnati tare da ‘yan majalisar jiha guda uku.

Mai shari’a Sika Aprioku ta yi fatali da karar da ke neman a tilasta wa gwamnan sake gabatar da kasafin kudin 2024 ga majalisar da Martin Amaewhule ke jagoranta.

Kara karanta wannan

Kwamitin kudirin haraji ya gana da malamai 120 domin neman goyon baya

Fubara da Wike
Fubara ya samu nasara a kotu kan mutanen Wike. Hoto: Sir Siminalayi Fubara|Nyesom Ezonwo Wike
Asali: Facebook

Rahoton Channels ya nuna wadanda suka shigar da karar sun bukaci gwamnan ya tura kasafin kudin ga 'yan majalisar 27.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotu ta ba gwamna Fubara gaskiya

Mai shari’a Sika Aprioku ta bayyana cewa gwamna zai iya aiki da majalisar da aka kafa bisa doka, kamar yadda tsohon gwamna Nyesom Wike ya yi aiki da ‘yan majalisa shida a lokacinsa.

Vanguard ta rahoto cewa Sika Aprioku ta bayyana cewa a lokacin Wike, ya yi amfani da 'yan majalisa da suke kasa da kashi biyu bisa uku na yawan mambobin majalisar.

A cewarta:

“Kamar yadda tsohon gwamna Ezenwo Nyesom Wike ya gabatar da kasafin kudi ga ‘yan majalisa shida kawai,
Haka kuma Gwamna Siminalayi Fubara zai iya mu'amala da majalisar da aka kafa bisa doka karkashin jagorancin Oko-Jumbo.”

Kotun ta kara bayyana cewa Fubara zai cigaba da aiki da 'yan majalisa ukun har sai kotun koli ta yanke hukunci kan matsalar hurumin 'yan majalisar 27 da suka rasa kujerunsu.

Kara karanta wannan

Farfesoshin Jami’ar ABU Zaria sun fito da illolin da ke cikin kudirin gyaran haraji

Dalilin watsi da karar mutanen Wike

Kotun ta yi karin haske bayan watsi da karar da ta bukaci gwamnan ya sake gabatar da kasafin kudin 2024 ga'yan majalisar 27.

Mai shari’a Aprioku ta bayyana cewa karar ba ta da tushe balle makama, kuma ba ta cancanci amincewa ba.

“Kiran da ake yi na sake gabatar da kasafin kudi ga tsoffin ‘yan majalisar 27, ba shi da wani tasiri kuma an yi watsi da shi.”

- Mai shari’a Aprioku

Kotu ta ci tarar mutanen Wike N500,000

Kotun ta umarci masu karar su biya gwamnatin jihar Rivers, gwamna Fubara, da babban lauyan jihar N500,000 a matsayin kudin bata lokaci.

Haka kuma kotun ta jaddada cewa, duk wasu nade-naden gwamnati da suka hada da nadin alkalan kotu da sauran manyan mukamai, za su kasance ne karkashin ‘yan majalisa ukun.

Wannan hukunci ya tabbatar da cewa Gwamna Fubara yana kan turba ta doka wajen gudanar da harkokin gwamnatin jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Tinubu na ganin sabuwar matsala daga Arewa, dattawa sun ƙi yarda da gyaran haraji

Dattawan Rivers sun ja kunnen Wike

A wani rahoton, kun ji cewa dattawan jihar Rivers sun ja kunnen ministan Abuja, Nyesom Wike kan maganganun da ya yi a kan Peter Odili.

Dattawan jihar sun bayyana cewa dole Wike ya fito ya ba Peter Odili hakuri matukar yana so a cigaba da zaman lafiya da ganin mutuncinsa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng