Yadda 'Yan Daba Suka Yi Jina Jina ga Sarki da Matarsa a gaban 'Yan Sanda

Yadda 'Yan Daba Suka Yi Jina Jina ga Sarki da Matarsa a gaban 'Yan Sanda

  • Wasu bata-gari sun kai hari kan fadar Sarkin al'ummar Halleluyah a Osun, Oba Jelili Olaiya, inda suka ji masa rauni
  • Sarkin ya ce akalla mutane hudu, ciki har da matarsa, sun ji rauni yayin harin, duk da cewa jami'an tsaro 18 sun kasance a fadar
  • Ana zargin cewa maharan sun zargi Sarkin da nada wani limami ba tare da izinin babban limamin garin Ido Osun ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Osun - Sarkin al'ummar Halleluyah a Jihar Osun, Oba Jelili Olaiya, ya yi karin bayani kan yadda wasu bata-gari suka kai hari fadarsa.

A yayin harin, an ji wa Sarkin da wasu mutane uku rauni, kuma an lalata wani bangare na fadarsa.

Jihar Osun
Basaraken Osun ya yi magana bayan 'yan daba sun masa duka. Hoto: Legit
Asali: Original

A wata hira da jaridar Punch Metro ta yi da shi, sarkin ya ce har yanzu yana asibiti, inda ake ci gaba da kula da shi sakamakon raunukan da ya ji.

Kara karanta wannan

Rigima ta barke tsakanin Sarki da wazirinsa a Arewa, lamarin ya kai ga bugun juna

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bata-gari sun zargi sarki da nada limami

A cewar Oba Jelili Olaiya, masu harin sun zarge shi da nada wani limami a cikin garin Ido Osun ba tare da izinin babban limamin garin ba, lamarin da ya fusata matasa, wanda hakan ya sa suka kai hari fadarsa.

Matasan sun mamaye fadar sarkin tare da lalata wasu kayan cikin fada, sannan suka yi wa mutane hudu rauni, ciki har da matar sarki.

Jami'an tsaro ba su hana hari ba inji sarki

Sarkin ya ce duk da kasancewar jami'an tsaro 18 a fadar lokacin harin, sun kasa dakile bata garin, ya ce jami'an sun hada da 'yan sanda da ma’aikatan hukumar tsaro ta NSCDC.

Oba Olaiya ya ce:

“Jami’an tsaro sun kasance a nan lokacin harin, amma abin takaici, ba su iya hana wannan hari mai muni ba. Har aka kai ga ji mana rauni, ciki har da mata ta da wasu mutane biyu.”

Kara karanta wannan

Matasa sun lakadawa basarake duka kan nada limamin Juma'a, an ceto rayuwarsa

Lamarin ya jawo damuwa kan yadda ake gudanar da tsaro a yankin, musamman a lokutan tashin hankali.

Sarkin na cigaba da samun kulawa a asibiti

Bayan harin, an garzaya da Oba Jelili Olaiya zuwa asibiti domin kula da raunukan da ya ji, sarkin ya ce har yanzu yana asibiti inda likitoci ke ba shi kulawa.

Sarkin ya yi kira ga hukumomin tsaro da su dauki matakin gaggawa domin tabbatar da cewa irin wannan hari bai sake faruwa ba a nan gaba.

Ya ce dole ne a tabbatar da doka da oda, kuma wadanda suka aikata aika-aikar su fuskanci hukunci.

Har yanzu ana jiran karin bayani daga hukumomin tsaro kan matakan da za su dauka domin magance wannan matsala da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankin.

An kashe 'yan sanda 140 a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar 'yan sandan birnin tarayya Abuja sun tabbatar da cewa an kashe mata jami'ai 140 a 2024.

Kara karanta wannan

Daga zuwa sasanta rikicin miji da mata, an kashe wani malamin addini a Najeriya

Kwamishinan 'yan sandan birnin tarayya Abuja ya bayyana zanga zanga da rashin lafiya cikin abubuwan da suka jawo mutuwar jami'an.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng