Hadimar Gwamnan Kaduna Ta Tsallake Rijiya da Baya a Hannun 'Yan Bindiga, Ta yi Bayani

Hadimar Gwamnan Kaduna Ta Tsallake Rijiya da Baya a Hannun 'Yan Bindiga, Ta yi Bayani

  • Mai taimakawa ta musamman ga Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna kan harkokin siyasa, Rachael Averick, ta fuskanci hari daga wajen ƴan bindiga
  • Hadimar gwamnan na jihar Kaduna ta tsallake rijiya da baya bayan an farknake ta a kan hanya bayan ta ƙaddamar da wani asibiti da aka gina
  • Rachael Averick ta yi bayanin cewa ta ritsa da rayuwarta kuma tana cikin ƙoshin lafiya, amma direbanta da wani ɗan sanda sun samu raunukan harbin bindiga

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Mataimakiya ta musamman kan harkokin siyasa ga gwamnan jihar Kaduna, Hon. Rachael Averik, ta tsallake rijiya da baya.

Hadimar ta Gwamna Uba Sani ta tsallake rijiya da bayan ne a wani yunƙurin kashe ta da aka yi a yankin Kudancin Kaduna.

An farmaki hadimar gwamnan Kaduna
Rachael Averick ta tsallake rijiya da baya Hoto: Senator Uba Sani, Rachael Averick
Asali: Facebook

Jaridar Leadership ta rahoto cewa Rachael Averick tana cikin ƙoshin lafiya, amma direbanta da wani ɗan sanda sun samu raunuka sakamakon harbin bindiga.

Kara karanta wannan

Ana batun tsadar mai, gwamnatin Sokoto ta samar da shirin saukaka zirga zirga

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda hadimar gwamnan Kaduna ta sha da ƙyar

Da take bayyana lamarin, Rachael Averick ta ce an kai mata harin ne a ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu, 2025, a tsakanin ƙauyukan Tsauni Majidadi da Gani a ƙaramar hukumar Sanga ta jihar Kaduna.

Mai taimakawa Gwamna Uba Sani na kan hanyarta ta zuwa Gwantu bayan ta ziyarci masarautar Arak domin ziyarar ta'aziyya, da ƙaddamar da wani asibiti da Alhaji Muhammad Umar Numbu ya gina.

Ta bayyana cewa ɗaya daga cikin jami’an ƴan sandan da ke tare da ita da direban motar sun samu raunuka a yayin artabu da maharan.

Rachael Averick ta bayyana cewa maharan sun buɗewa motar da suke ciki ne wuta.

Masu amfani da yanar gizo sun yi Allah wadai da yunkurin kisan gillar da aka yi wa Rachael tare da yi mata addu'ar ci gaba da samun kariya.

An yi mata jaje

Williams Moses:

"Duniya akwai mugunta. Allah ya ci gaba da baki kariya honorabul. Ina musu fatan samun sauƙi cikin gaggawa."

Kara karanta wannan

Fadan Fulani da makiyaya ya barke a Jigawa, an samu asarar rayuka

MC Flows Edofugarboy:

"Aa meyasa ake samun irin haka a Kudancin Kaduna, wannan ba abu ba ne mai kyau, abin da muke buƙata shi ne ƙauna, babu buƙatar cutar da mutane masu nagarta."
"Honarabul tana da kirki, Allah ya ci gaba da kare ta a duk inda ta samu kanta a ciki."

Kande Ibrahim:

"Kai, ba ɗaɗi. Ina yi wa waɗanda suka samu raunuka fatan samun sauƙi."

Kefas James:

"Wannan babban abu ne. Allah ya sanya ta tsira, ina yi wa waɗanda suka jikkata fatan samun sauƙi cikin gaggawa."

Abdulmajid Garba:

"Allah ya tsare gaba sauran Allah ya basu lafiya"

Mary John:

"Mun godewa Allah da kuka tsira. Ina yi musu fatan samun sauƙi cikin gaggawa. Allah ya ci gaba da kare ku daga dukkanin sharri."

Sanatan Kaduna ya sha da ƙyar

A wani labarin kuma, kun ji cewa sanatan da ke wakiltar Kaduna ta Tsakiya, ya tsallake rijiya da baya bayan an kai masa wani hari.

Kara karanta wannan

"Babu sauran sansanin ƴan bindiga a jihata," Gwamna a Arewa ya cika baki

Sanata Lawal Adamu Usman ya bayyana cewa wasu mahara sun yi yunƙurin kashe shi, amma da yake akwai sauran ragowar numfashinsa, ya samu ya kuɓuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng