Karshen Shekara: NDLEA Ta Tafka Kwamushe a Legas da Kano, an Kame Fitaccen Dan Fim
- Hukumar hana sha da fataucin kwayoyi ta NDLEA ta bayyana manyan ayyukan da ta yi a karshen shekarar 2024
- An kama mutanen da ake zargin suna da hannu wajen shigo da kayan maye a Najeriya, musamman a jihohi Legas da Kano
- Shugaban NDLEA ya mika sako ga ‘yan Najeriya, ya bayyana abin da hukumar ta sanya a gaba a lokaci irin wannan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Najeriya - Hukumar Yaki da Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta fara shekarar 2025 da gagarumin nasara a hare-haren da ta ke yi a fannin miyagun kwayoyi.
A ranar 1 ga watan Janairu, 2025, jami’an hukumar sun cafke Alhaja Aishat Feyisara Ajoke Elediye, wadda aka fi sani da suna “Iya Ruka,” a cikin gidanta da ke Okota, Legas.
An yi wannan kamun ne bayan an kama mota dauke da miyagun kwayoyi da ma’aikatan ta ke jigila, wanda ya kunshi kilo 1,540 na tabar wiwi da aka shigo da su daga kasashen waje.
A baya ana zargin Aishat da safarar kwaya
Wannan babban nasara na NDLEA ya kawo karshen shekaru da dama na zarge-zarge kan Aishat Elediye wadda ake zargin tana jagorantar wata babbar kungiya ta fataucin miyagun kwayoyi, musamman a yankin Mushin na Legas.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Alhaja Ajoke, wadda ta shahara a matsayin mai kasuwancin kayan ado da tufafi daga kasar Sin, ta dade tana kin bayyana asalin aikin da take yi, wanda ake zargi yana da alaka da safarar miyagun kwayoyi.
Bayan da aka kama ta, an tsare ta tare da wani abokin aikinta da ke kula da jigilar kwayoyin a yankuna daban-daban.
An kama Emeka Mbadiwe a Legas
A wani hari na daban, jami’an NDLEA sun kama shahararren dan fim, Emeka Emmanuel Mbadiwe, a dakin otel dinsa da ke Lekki a ranar 27 ga Disamba, 2024.
Mbadiwe ya shiga hannu ne bayan an kama abokin aikinsa, Uzoekwe Ugochukwu James, a lokacin da yake karbar kaya dauri 33 na tabar wiwi mai nauyin kilo 17 daga kasar Amurka.
Wannan kwayoyi sun kasance cikin kwalaye na katako da aka kawo su Najeriya ta hanyar tashar jiragen sama ta Murtala Muhammed da ke Legas.
Kamun matasa a da karkar kwaya a Kwara
A jihar Kwara, hukumar NDLEA ta kama matashiya mai suna Khadijat Abdulraheem, mai shekaru 24, da kuma wani dalibi mai suna Ayomide Morakinyo, mai shekaru 20.
Ana zargin matasan ne da laifin hada kai da sayar da kek da aka sa kwayoyi a cikinsu domin tallatawa matasa.
An bankado kek kanana guda 42 da ke dauke da miyagun kwayoyi a cikin gidansu bayan an gudanar da bincike.
Babban kamun da aka yi a Port Harcourt da Kano
A ranar 31 ga Disamba, 2024, jami’an NDLEA tare da hadin gwiwar wasu jami’an tsaro sun yi babban kamun maganin tari mai suna codeine a tashar jiragen ruwa ta Port Harcourt, inda aka samu kwalaben maganin tari fiye da 316,800.
Hakanan a Kano, an kama kwayoyi guda 149,090 na Tramadol da Exol-5 daga hannun wani dillali a cikin wata shahararriyar kasuwa na jihar ta Kano.
Sakon shugaban NDLEA ga ‘yan kasa
Shugaban hukumar NDLEA, Brig. Gen. Mohamed Buba Marwa (Rtd), ya bayyana jin dadinsa game da nasarorin da jami’an hukumar suka samu.
Ya bayyana cewa dabarun da ake bi na tabbatar da ingantaccen aiki tsakanin jami’an tsaro da sauran hukumomin da ke yaki da fataucin kwayoyi, suna taimakawa wajen rage yawan miyagun kwayoyi a cikin kasar.
Haka kuma, ya jaddada muhimmancin faukar matakan hana sha da fataucin miyagun kwayoyi don kare rayukan matasa da kuma tabbatar da zaman lafiya a kasar.
Asali: Legit.ng