Ta Ku Ta Kare: Sojoji Sun Shirya Tsaf Za Su Ga Karshen ’Yan Ta’addan Najeriya a 2025

Ta Ku Ta Kare: Sojoji Sun Shirya Tsaf Za Su Ga Karshen ’Yan Ta’addan Najeriya a 2025

  • Shugaban hafsun tsaron Najeriya ya bayyana kwarin gwiwar soji na tabbatar da tsaro a shekarar da aka shiga ta 2025
  • Ya ce a wannan shekarar babu wata kafa ko kofa da sojoji za su bari don ta’adda su rintsa, sai an tabbatar da tsaron kasa
  • An jima ana fama da matsalar tsaro a Najeriya, lamarin da ke kara tabarbarewar lamurra, musamman kasuwanci da asarar rayuka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Jihar Plateau - Shugaban Hafsun Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya bayyana cewa babu wurin tsira ga 'yan ta'adda a kasar nan a shekarar 2025.

Ya yi wannan furuci ne yayin ziyarar da ya kai wa dakarun sojoji a karamar hukumar Mangu ta jihar Plateau.

Janar Musa ya jaddada kudirin rundunar soji na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin 'yan Najeriya.

Shugaban soji ya sha alwashin karar da su Turji
Za a kawo karshen 'yan ta'adda a 2025 inji shugaban soji | Hoto: Defense HQ
Asali: Getty Images

Kokarin soji na inganta tsaro a Najeriya

Ya ce gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yaki da ta'addanci, tare da tabbatar da cewa dakarun sun samu dukkan kayan aikin da suka dace domin cimma wannan buri.

Kara karanta wannan

"An shiga wahala bayan zaben Tinubu," Sanatan APC ya fadi manufar gwamnati

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani taro da aka yi a baya-bayan nan, Janar Musa ya yi kira ga sabbin manyan jami'an da aka kara wa girma da su dauki matakan kakkabe 'yan ta'adda da masu satar man fetur.

Ya ce lokaci ya yi da za a kawo karshen wannan matsala da ta addabi kasar nan fiye da shekaru goma sha biyar, AIT ta ruwaito.

Kira ga jama'a su guji mu'amala da 'yan ta'adda

Haka kuma, shugaban tsaron ya gargadi al'ummar kasar nan da su guji yin hulda da 'yan ta'adda ko masu garkuwa da mutane, domin hakan na kara dagula lamarin tsaro, inji PM News.

Ya ce yin hakan zai taimaka wajen rage karfin 'yan ta'adda da kuma tabbatar da zaman lafiya a yankunan da abin ya shafa.

Janar Musa ya nuna kwarin gwiwa cewa shekarar 2025 za ta zama shekara mai muhimmanci wajen kawo karshen ta'addanci a Najeriya, tare da yin kira ga dakarun soji da al'ummar kasa su hada kai domin cimma wannan buri.

Kara karanta wannan

Tinubu: Kalaman Peter Obi sun yi wa APC zafi, ta zarge shi da son tunzura jama'a

Yadda ake fama da matsalar tsaro a Arewa

Jihohin Arewacin Najeriya ne suka fi samun matsala a fannin da ya shafi tsaro, inda ake yawan kashe mutane tare da sace dukiyoyinsu.

Arewa maso Gabas na fama da barnar 'yan ta'addan ISWAP da Boko Haram, wadanda suka shafe shekaru kusan 15 suna barna.

A Arewa maso Yamma, an fi fuskantar satar shanu da kuma garkuwa da mutane, inda ake karbar kudin fansa tare da kashe mutane ba gaira ba dalili.

Sojoji sun kuduri ganin bayan Bello Turji

A wani labarin kuma, kun ji yadda shugaban tsaron ya yi alkawarin kawo karshen dukkan wasu ‘yan ta’adda da ke tayar da zaune tsaye a cikin Najeriya.

Babban hafsan tsaron ya yabawa gwarazan sojojin bisa sadaukarwa da jajircewar da suke yi a harkar tsaron kasa tare da tabbatar masu za a inganta walwalarsu.

Ya kuma bukaci sojoji da su kasance masu taka tsan-tsan da kwarewa wajen kare kasa da kuma mutunta hakkin dan Adam wajen gudanar da ayyukansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.