Mummunar Gobara Ta Tashi a Fitacciyar Kasuwa, an Samu Asarar Dukiya Mai Yawa
- Mutane da dama sun shiga halin jimami bayan mummunar gobara ta jawo musu asarar dukiya mai yawa a jihar Sokoto da ke yankin Arewa maso Gabas
- Mummunar gobarar wacce ta tashi a fitacciyar kasuwar Kara da ke Sokoto ta lalata shaguna masu yawa da jawo asarar dukiyar miliyoyin naira
- Jami'an hukumomin ba da agaji na SEMA da NEMA sun ziyarci kasuwar tare da ba da tabbacin tallafi ga mutanen da gobarar ta jawo musu asara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Sokoto - An samu tashin wata mummunar gobara a fitacciyar kasuwar hatsi ta Kara da ke jihar Sokoto.
Gobarar wacce ta tashi da safiyar ranar Asabar, 4 ga watan Janairun 2024 ta yi ɓarna inda ta lalata hatsi da kadarori na miliyoyin naira.
Gobara ta yi ɓarna a fitacciyar kasuwa a Sokoto
Jaridar The Punch ta rahoto cewa gobarar wacce ta auku a kasuwar, ta lalata sama da shagunan niƙa 50.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gobarar ta kuma shafi gidajen mutane da dama da suke makwabtaka da fitacciyar kasuwar, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Duk da cewa har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba, lamarin ya janyo asarar dukiya ga waɗanda abin ya shafa, inda aka ƙiyasta asarar za ta haura Naira miliyan 50.
Gobarar ta lalata kayayyakin abinci da suka haɗa da shinkafa, gero, wake, da kuma buhunan wasu kayayyaki da aka ajiye domin kasuwanci.
Ƴan kasuwa sun yi asara
Daga cikin mutanen da gobarar ta shafa har da Glory Matthew Abba, wata mai shagon da ta yi asarar injin niƙa, wanda kuɗinsa ya kai Naira miliyan 1.8.
Wani da lamarin ya shafa, Aliyu Achida, ya yi asarar gidansa da kayan amfanin gona da suka haɗa da shinkafa, gero, da wake, inda ya yi asarar kusan Naira miliyan uku.
Jami'ai sun je gani da ido
Jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa ta jihar Sokoto (SEMA) da hukumar bayar da agajin gaggawa ta ƙasa (NEMA) sun je kasuwar domin gani da ido kan irin ɓarnar da gobarar ta yi.
Jami’an hukumomin sun ziyarci wuraren da suka lalace a kasuwar Kara, domin tantance halin da ake ciki tare da jaddada aniyarsu ta bayar da tallafi ga mutanen da gobarar ta shafa.
Daraktan ba da agaji na hukumar SEMA, Mustapha Umar, ya ce ana gudanar da bincike kan tashin gobarar.
"Ana ci gaba da gudanar da bincike kan musabbabin gobarar, kuma hukumomi na kira ga jama’a da su sanya ido tare da kai rahoton duk wata alamar gobara a kusa da su."
- Mustapha Umar
Gobara ta lalata shaguna masu yawa
A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu tashin wata mummunar gobsrana ɗaya daga cikin manyan kasuwannin da ake ji da su a jihar Nasarawa da ke yankin Arewa ta Tsakiya na Najeriya.
Mummunar gobarar wacce ta tashi a fitacciyar kasuwar Masaka da ke ƙaramar hukumar Kauru ta jihar, ta jawo asarar dukiya mai tarin yawa.
Gobarar ta ƙona shaguna masu tarin yawa tare da lalata dukiya ta miliyoyin naira.
Asali: Legit.ng