Za a Sha Jar Miya: Yadda Talakawa da Ma’aikata Za Su More Idan Aka Yarje da Kudurin Haraji
- Gwamnatin Tinubu ta bayyana babban abin da ta tanadarwa ‘yan Najeriya a gyaran kudororin haraji da ta gabatar
- ‘Yan Arewa sun bayyana kukansu, inda suke zaton za a mayar da jihar Legas shalele idan aka kaddamar da shirin
- Sai dai, rahoto ya bayyana hanyoyi da dama da za su amfani ma’aikata da kananan ‘yan kasuwa da ma talakawan kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Najeriya - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa sabbin kudirorin gyaran haraji za su inganta rayuwar ma'aikata a Najeriya.
Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan Tsare-tsaren Kudin Gwamnati da Tsara Haraji, Taiwo Oyedele, ya ce ma'aikatan da ke samun kusan Naira miliyan daya a shekara (kimanin N83,000 a wata) za su sami 'yanci daga biyan harajin PAYE.
Wannan zai amfani kusan kashi daya bisa uku na ma'aikatan gwamnati da masu zaman kansu a fadin Najeriya.
Masu babban albashi ma za su more
Ga masu samun matsakaicin albashi, wadanda ke karbar albashi har zuwa N20m a shekara (kimanin N1.7 miliyan a wata), za a rage musu yawan harajin PAYE.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewarsa, wannan zai amfani karin kashi 60% na ma'aikatan Najeriya. Haka kuma, sojojin da ke aikin yaki da rashin tsaro za su sami 'yanci daga biyan harajin na PAYE.
Domin rage tsadar rayuwa, an shirya cire Harajin Kayayyaki (VAT) daga kayan masarufi kamar abinci, kiwon lafiya, da ilimi, wadanda ke cinye kusan kashi 60% na abin da gidaje ke amfani da kudinsu a Najeriya.
Za a cire haraji a fannin sufuri dss
Hakanan, fannin sufuri, makamashin hasken rana, iskar gas ta CNG, kayan jarirai, kayan tsafta jiki, da man fetur duk sun fita daga VAT.
Rahoto ya bayyana cewa, wadannan kashe kudi su ke wakiltar sama da kashi 20% na abin da ake kashewa a gidaje a Najeriya.
Wannan zai taimaka wajen rage nauyin kudi ga iyalai, musamman masu karamin karfi da ma’aikata a fadin kasar.
Ta yaya sabon kudurin zai shafi albashi?
Kudurorin gyaran harajin sun hada da tanade-tanade don karfafa biyan albashi mai kyau ga ma'aikata, ciki har da rangwamen haraji da karin albashi da tallafin sufuri ga masu karamin albashi.
An kuma shirya janye VAT daga gidajen haya da sayen gidaje domin karfafa samun gidaje masu sauki.
Za kuma a cire harajin hatimi na gwamnati daga hayar da ta yi kasa Naira miliyan 10 domin rage nauyin kudi ga masu neman haya a kasar.
Alfanun sabon kudurin ga ayyukan yi
Gyaran harajin dai ya mayar da hankali ne kan kirkirar ayyukan yi ta hanyar ba da rangwamen haraji ga masu daukar ma'aikata da yawa, kirkirar dokoki masu sauki don jawo ayyukan nesa ga 'yan Najeriya, da cire kashi 97% na Kananan da Matsakaitan Kamfanoni (SMEs) daga biyan haraji.
Sai dai, har yanzu ‘yan Najeriya, musamman ‘yan Arewa na yiwa wannan tsarin na Tinubu bahagon fahimta, lamarin da ke kara daukar hankali a kasar.
Malaman addini da masu fada a aji a Arewacin Najeriya sun yi martani a lokuta da yawa kan wannan kuduri na shugaban kasa Najeriya Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Legit.ng