Dattawa Sun Bukaci Yiwa Sanatan PDP Kiranye, Sun Bayyana Dalilansu

Dattawa Sun Bukaci Yiwa Sanatan PDP Kiranye, Sun Bayyana Dalilansu

  • Ƙungiyar dattawan Kaduna ta Tsakiya sun buƙaci sanatan da ke wakiltarsu, Sanata Lawal Adamu da ya dawo gida
  • Dattawan sun bayyana cewa sanatan bai cika alƙawuran da ya ɗauka ba a yayin yaƙin neman zaɓen shekarar 2023
  • Sun kuma yi tantamar iƙirarin kashe shi da sanatan ya yi, inda suka zarge shi da kunyatasu a bainar jama'a

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Kungiyar dattawan Kaduna ta Tsakiya ta buƙaci a yi wa Sanata Lawal Adamu Usman, sanata mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Tsakiya kiranye, biyo bayan zargin kashe shi da ya yi cikin 'yan kwanakinnan nan.

Dattawan sun bayyana cewa rashin cika alƙawuran da Sanata Lawal ya ɗauka yayin yaƙin neman zaɓe, na daga cikin manyan dalilan da suka sanya su bijiro da batun kiranyen.

Kara karanta wannan

Fadan Fulani da makiyaya ya barke a Jigawa, an samu asarar rayuka

Dattawan Kaduna za su yi wa Sanata Lawal Adamu Usman Kiranye
Dattawan Kaduna ta Tsakiya za su dawo da Sanata Lawal Adamu Usman Gida. Hoto: Sen Lawal Adamu Usman
Asali: Facebook

A rahoton jaridar Vanguard, ƙungiyar dattawan ta bayyana cewa a tarihin Sanatocin da suka taɓa yi a baya, babu wani sanata da ya gaza kama hanyar sauke nauyinsa kamar Sanata Lawal Adamu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dattawa sun buƙaci dawo da Sanata Lawal gida

Ƙungiyar ta buƙaci a dawo da Sanatan gida a cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun shugabanta, Alhaji Inuwa Bala Rigasa, inda ta bayyana rashin jin ɗadinta game da iƙirarin da ya yi na neman kashe shi da kuma rashin nemowa talakawan yankinsa haƙƙunansu.

Dattawan sun bayyana cewa Sanatan wanda ya samu nasarar lashe zaɓen kujerar Majalisar Dattawa ta Kaduna ta Tsakiya a shekarar 2023, ya tayar mu su da hankali kan iƙirarin da ya yi, duba da cewa babu wata hujja da ke tabbatar da hakan.

A wani rahoto da jaridar Dailytrust ta wallafa, an bayyana cewa Sanata mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta tsakiya, Lawal Adamu Usman, ya tsallake rijiya da baya a wani yunkurin kashe shi da aka yi.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya ɗebo ruwan dafa kansa da ya taɓa ƙimar Atiku, matasa sun masa rubdugu

Har yanzu ba a tabbatar da gaskiyar iƙirarin harin ba

Sai dai ƙungiyar dattawan ta bayyana cewa rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce har yanzu ba ta samu wani korafi a hukumance daga Sanatan ba, baya ga abinda ya wallafa a shafukan sada zumunta.

“Abu mafi muni, mun ji kunya matuƙa a lokacin da Sanata Lawal Adamu ya wallafa cewa wasu ‘yan daba sun kai masa hari a lokacin bikin sabuwar shekara.”
“Mun kafa kwamitin bincike don tabbatar da sahihancin ikirari harin, kuma har zuwa lokacin da muka fitar da wannan sanarwar, babu wata hukuma ta ‘yan sanda ko wasu al'ummar Kawo da suka tabbatar da faruwar lamarin.”
"A wannan gaɓa, ba za mu iya karɓar uzurinsa ba don haka ne ma muka nemi gaggauta yi ma sa kiranye daga Majalisar Dattawan."

- Alhaji Inuwa Bala Rigasa

El-Rufai ya ziyarci tsohon ma'aikacinsa a gidan yari

Kara karanta wannan

Tsohon jami'in gwamnatin El Rufai ya shiga hannun jami'an tsaro a Kaduna

A wani rahoto da muka wallafa a baya, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ziyarci tsohon shugaban ma'aikatansa Bashir Saidu da ke tsare a gidan gyaran hali.

Ziyarar ta El-Rufai na zuwa ne dai jim kaɗan bayan da wata kotun majistare ta ba da umarnin tsare Bashir a gidan gyaran hali saboda zargin almundahana.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng