Ajali Ya Yi: Sarki a Najeriya Ya Gamu Mummunan Hatsari, Allah Ya Yi Masa Rasuwa
- Gwamnan jihar Bayelsa, Douye Diri ya mika sakon ta'aziyya bisa rasuwsr dsrkin Ofoni, Mai msrtaba Auditor Onakpohor
- Basaraken ya rasa ransa ne a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi a hanyar zuwa kai wa gwamnan ziyarar barka da shigowar 2025
- A wata sanarwa da mai magana da yawunsa ya fitar yau Asabar, gwamnan ya jajantawa sauran waɗanda suka samu rauni a hatsarin
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Bayelsa - Sarkin Ofoni da ke ƙaramar hukumar Sagbama a jihar Bayelsa, Mai martaba Auditor Onakpohor ya riga mu gidan gaskiya ranar Juma'a.
Basaraken wanda ake kira da Amananaowei na Ofoni ya rasa rayuwarsa ne a wani mummunan hatsarin mota da ta rutsa da shi a jihar Bayelsa.
Gwamna Douye Diri ya nuna takaici da alhinin rasuwar sarkin sakamakon hatsarin da ya faru a titin Sagbama-Ekeremor, rahoton Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda sarkin ya rasu a hatsarin mota
Hatsarin ya faru ne a lokacin da motar da ke dauke da HRH Onakpohor da wasu sarakunan kimanin 12 ta kucce, ta sauka daga titin sannan ta yi cikin daji a kusa da Sagbama.
Rahoto ya nuna nan take aka kwashi waɗanda ke cikin motar gaba ɗaya zuwa babban asibitin Sagbama domin ba su agajin gaggawa.
Waɗanda kuma suka ji munanan raunuka an wuce da su zuwa babban asibitin koyarwa na jihar Delta da ke Okolobiri.
Sarkin na Ofoni wanda ya rasu yana cikin tawagar Sanatan Bayelsa ta yamma, Cif Henry Seriake Dickson a hanyar zuws gidan Gwamna Douye Diri a mahaifara.
Gwamna Diri ya miƙa sakon ta'aziyya
Mai magana da yawun gwamnan, Daniel Alabrah ya ce Gwamna Diri ya soke ziyarar nan take bayan samun labarin hatsarin da kuma mutuwar sarkin.
A wata sanarwa da ya fitar yau Asabar, Alabrah ya ce:
“Gwamna Diri ya samu labari daga bakin mataimakinsa, Sanata Lawrence Ewhrudjakpo wanda shi ma dan asalin Ofoni ne.
"Kuma a madadin gwamnatin jihar Beyelsa, yana mika ta’aziyya ga iyalan sarki da al’ummar Ofoni. Ya kuma jajantawa waɗanda suka samu rauni tare da fatan Allah ya tashi kafaɗunsu."
"Gwamnan Diri ya kuma jajantawa magabacinsa, Sanata Dickson, wanda shi ne shugaban tawagar."
Tsohon dogarin Jonathan ya kwanta dama
A wani rahoton, kun ji cewa Moses Jituboh, tsohon dogarin Goodluck Jonathan ya mutu yana da shekara 54 a duniya.
Marigayi tsohon mataimakin bsbban Sufetan ƴan sanda ƙasa ya mutu ne bayan yar gajeriyar jinya, sn ce za yi binciken gawa don gano abin da ya zama ajalinsa.
Asali: Legit.ng