Gwamnan da Ake Raɗe Raɗin Zai Nemi Takarar Shugaban Kasa a 2027 Ya Kafa Tarihi
- Gwamna Seyi Makinde ya yi wasu sababbin naɗe-naɗen da ba a taɓa yin irinsu ba a tarihin gwamnatin jihar Osun
- Gwamnan na PDP, wanda a kwanakin baya aka yaɗa jita-jitar yana shirin neman takarar shugaban kasa a 2027, ya naɗa manyan sakatarori 45
- Kwamishinan yaɗa labarai na Oyo ya ce wannan ne karon farko da aka taba yin haka, ya ce gwamnan ya shirya inganta walwalar ma'aikata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Oyo - Gwamna Seyi Makinde, ya yi wani gagarumin yunkuri da nufin inganta harkokin gwamnatinsa a jihar Oyo.
Gwamna Makinde ya amince da naɗin sababbin manyan sakatarori guda 45 tare da sakatarorin zartarwa guda uku a gwamnatinsa.
Gwamna ya naɗa manyan sakatarori 45
Kwamishinan yaɗa labarai na jihar Oyo, Dotun Oyelade ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a, 3 ga watan Janairu, Tribune Nigeria ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar na kuma ɗauke da sa hannun shugabar kula da harkokin ma'aikatan gwamnatin Oyo, Mrs. Olubunmi Oni.
"Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo ya amince da nadin manyan sakatarorin dindindin guda 45 da sakatarorin zartarwa uku," in ji sanarwar.
Yadda gwamnan ya raba manyan sakatarorin
Mutum 16 daga cikin sababbin manyan sakatarorin dindindin ɗin da Gwamna Makinde ya nada za su yi aiki ne a ma'aikatun gwamnati.
Sai kuma masu sa ido kan harkokin ilimi guda shida, manyan sakatarori shida a fannin kiwon lafiya da wasu manyan sakatarori bakwai a ma'aikatar kananan hukumomi.
Kwamishinan yaɗa labarai ya ce:
"Wannan sabon nadin mukamai ba a taba yin irinsa ba, ya saɓawa yadda aka saba a baya, inda aka keɓe naɗa manyan sakatarorin a ma'aikatan gwamnati kaɗai."
Gwamna Makinde zai farantawa ma'aikata
Oyelade ya jaddada kudirin Gwamna Makinde na inganta walwala da jin dadin ma’aikata a jihar Oyo, kamar yadda jaridar Guardian ta ruwaito.
A cewarsa, gwamnatin Makinde ta dauki ma’aikata sama da 23,000 kuma albashin da take biya ya haura Naira biliyan 143 a shekara.
Ana raɗe-raɗin Makinde zai nemi shugabancin ƙasa
Kun ji cewa Gwamna Seyi Makinde ya yi magana kan raɗe-raɗin da ke yawo a sohiyal midiya cewa zai nemai takarar shugaban ƙasa a 2027.
Makinde ya ce a yanzu ya maida hankali ne wajen sauke nauyin da al'umma suka ɗora masa, inda ya kara da cewa ya yi wuri a fara tunanin takara a 2027.
Asali: Legit.ng