Obasanjo Ya Taso Kamfanin NNPCL a Gaba, Ya Fadi Cin Mutuncin da Aka Yi Masa

Obasanjo Ya Taso Kamfanin NNPCL a Gaba, Ya Fadi Cin Mutuncin da Aka Yi Masa

  • Tsohon shugaban ƙasan Najeriya, Olusegun Obasanjo, ya yi magana kan gayyatar da kamfanin NNPCL ya yi masa kan duba matatun man da aka gyara
  • Olusegun Obasanjoɓya caccaki gayyatar wacce ya bayyana a matsayin mutuntawa ga ofishinsa da shi kansa
  • Tsohon shugaban ƙasa ya nuna cewa kamfanin NNPCL bai rubuta masa a hukumance cewa yana gayyatarsa domin zuwa gani da ido a matatun

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Ogun - Tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi martani kan gayyatar da kamfanin NNPCL ya yi masa.

Olusegun Obasanjo ya yi Allah-wadai da gayyatar da kamfanin na NNPCL ya yi masa kan duba matatun man Port Harcourt da Warri, inda ya bayyana hakan a matsayin rashin mutuntawa.

Obasanjo ya soki gayyatar da NNPCL ya yi masa
Obasanjo ya caccaki NNPCL kan gayyatarsa Hoto: NNPC Limited, Zainab Nasir Ahmad
Asali: Facebook

Da yake mayar da martani ga gayyatar a wata hira da jaridar The Punch, Obasanjo ya ce irin wannan gayyata na nuna rashin mutunta ofishinsa da kuma shi kansa.

Kara karanta wannan

NNPCL ya fara gyaran matatar Kaduna, za a fara aikin tace mai a Arewacin Najeriya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamfanin NNPCL dai ta ta bakin mai magana da yawunsa, Olufemi Soneye, ya gayyaci tsohon shugaban ƙasar zuwa rangadin matatun man Port Harcourt da Warri.

Gayyatar kamfanin ta biyo bayan wata hira da aka yi da Obasanjo, inda tsohon shugaban ƙasar ya bayyana yadda aka kasa mayar da matatun man Najeriya hannun ƴan kasuwa.

Obasanjo ya caccaki kamfanin NNPCL

Obasanjo ta bakin mai taimaka masa kan harkokin yaɗa labarai, Kehinde Akinyemi, ya bayyana cewa kamfanin bai aika masa da wata gayyata a hukumance ba har zuwa ranar Alhamis, 2 ga watan Janairu, 2024.

"Shin haka ya dace a gayyaci tsohon shugaban ƙasa? Wa ya ce Baba ma ya ga maganar ko ya karanta labarin? Wannan rashin mutuntawa ne ga ofishin tsohon shugaban ƙasa."
"Ku tambayi NNPCL cewa har zuwa ranar 2 ga watan Janairu, sun tuntuɓe shi? Ko akwai wata takarda a hukumance da aka aika masa, ta gayyatarsa zuwa matatar man?"

Kara karanta wannan

Yadda tsohon shugaban Amurka ya ceci rayuwar Obasanjo har ya rayu zuwa yanzu

"Wannan babban cin fuska ne, kuma tsohon shugaban ƙasar ba zai iya girmama irin wannan da martani ba."

- Kehinde Akinyemi

Wane martani kamfanin NNPCL ya yi?

Ƙoƙarin jin ta bakin mai magana da yawun bakin kamfanin NNPCL, Olufemi Soneye, ya ci tura.

An kira sa sau uku tare da aika masa da sakonnin tes da WhatsApp domin tambayar ko da gaske ne kamfanin ya gayyaci tsohon shugaban ƙasar a hukumance.

Sai dai Soneye bai amsa kiran da aka yi masa ba, kuma bai dawo da amsar saƙonnin da aka tura masa har zuwa lokacin kammala haɗa wannan rahoton.

Obasanjo ya gano matsalar Najeriya

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi magana kan tarin matsaloli da ƙalubalen da ƙasar nan ke fuskanta.

Olusegun Obasanjo ya ɗora alhakin matsalolin da suka dabaibaye ƙasar nan a kan shugabanni da mabiyansu, inda ya ce sune suka haddasa komai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng