Peter Obi Ya Ziyarci IBB, Ya Bayyana Abubuwan da Suka Tattauna a kan Najeriya
- Tsohon dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar LP, Peter Obi ya ziyarci tsofaffin shugabanni a Najeriya don karfafa alaka
- Ya ziyarci tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, ya bayyana irin muhimmancin shawarwarinsa
- Mista Obi ya ce akwai bukatar a samar da sabuwar Najeriya, wacce ya ke ganin za a iya cimmawa idan aka yi aiki tare
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Niger - Tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, ya ziyarci Minna, babban birnin jihar Neja, don ganawa da wasu manyan shugabanni.
Mista Peter Obi ya bayyana cewa guda daga cikin dalilan ziyarar shi ne tabbatar da jajircewarsa ga gina kasa da hadin kan al’umma.
A cikin sakonni daban-daban da ya wallafa a shafinsa na X, Obi ya bayyana cewa ya fara ziyartar tsohon Shugaban kasa a lokacin soji, Janar Ibrahim Badamasi Babangida, a gidansa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi ya yabi Janar IBB
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Obi ya bayyana Janar Ibrahim Badamasi Babangida a matsayin uba ga kowa.
Mista Obi ya ce;
“Basirar Janar Babangida da fahimtarsa suna da matukar muhimmanci. Ina matukar godiya da damar da nake samu na ziyartarsa domin jin shawarwarinsa masu cike da hikima.”
Obi ya ziyarci tsohon gwamnan jihar neja
Mista Peter Obi ya bayyana cewa ya ziyarci tsohon gwamnan Neja, Dakta Mu’azu Babangida Aliyu domin kara dankon hadin kai.
Ya kara da cewa:
“Tattaunawarmu ta mayar da hankali kan muhimmiyar aikin gina kasa da kuma hakkinmu na bai daya wajen samar da kyakkyawar makoma ga kasarmu.”
Ya kara da cewa idan aka samu hadin kan da ya dace, za a iya cimma manufar samar da Najeriya sabuwa, wacce kowane dan kasa zai mora.
Jam'iyyar APC ta caccaki Peter Obi
A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Peter Obi ya jawo martanin APC bayan ya caccaki salon mulkin gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Jam'iyya mai mulki, ta bakin sakataren yada labaranta na kasa, Felix Morka ya gargadi Peter Obi da ya rika lura da kalamansa kar ya harzuka talakawa a lokacin da Tinubu ke kokari.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng